Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

  • Wani dan jarida dan asalin kasar Zambia, Anothony Mukwita ya yi matukar mamaki bayan ganin wani ya kusa kammala gini a cikin filinsa
  • Take a nan mutumin ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa shekarunsa 10 a kasar waje, dawowarsa ke da wuya ya ga wannan abin mamakin
  • Nan da nan mutane su ka fara ba shi shawarar nemo wanda ya ke ginin a filin don ya sayar masa, don kowa ya karu da kowa kuma a warware matsalar

Wani fitaccen dan jarida dan asalin kasar Zambia, Anthony Mukwita, bai dade da dawowa gida ba daga kasar waje bayan ya kwashe shekaru 10 a can.

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu
Yadda Anthony ya dawo daga kasar waje ya tarar wani ya tayar da ginin katafaren gida a filinsa. Hoto: Photos: Anthony Mukwita
Asali: Facebook

Marubucin ya rike kujerar jakada a ofishin jakadancin kasar Zambia na Stockholm da ke Sweden inda ya zauna tare da matarsa, Elaine da yaransa biyu, Lubinda da Lushomo.

Kara karanta wannan

Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

An kwace masa fili

Yayin da ya ke murnar ganin shagalin kirsimeti yana cike da shauki sai ya kai ziyara daya daga cikin filayensa ya tarar har wani ya mallake.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga dukkan alamu mutumin ya yi amfani da damar rashin zamansa a kasar inda ya bunkasa wurin ya tayar da gini.

Wanda ya samu jinjina ta musamman a kan bincike na harkar jarida na bankin duniya, ya ce shi da matarsa Elaine sun sha mamaki bayan kai ziyara Kabangwe.

Kamar yadda ya ce:

“Wani mutum mai wayau ya kusa kammala ginin gida mai dakuna hudu a filin da muka siya da sunan ni da matata. Idan kai ne hakan ta faru da kai ya zaka yi? "

Nan da nan mutane su ka fara ba shi shawarar a kan sayar wa mutumin filin

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

Mutanen kafafen sada zumunta sun fara ba tsohon darektan jaridar Zambia Daily Mail shawarar neman mutumin don sayar masa da filin ta yadda duk za su ci moriyar junayensu.

Akwai wadanda su ka ce ya nisanci filinsa ne hakan ya sa wani ya kalle wurin a matsayin yasasshe don haka wani ya mallake ya tayar da gini.

Wani Musunga Mushinge ya ce:

“Ku shirya ta hanyar sayar masa da filin a darajar wurin na yanzu sakamakon irin rashin dadin da ya sa ka ji a halin yanzu. Ka ga dukan ku kun amfana.”

Charity Mphande:

“Ka gode wa mutumin a kan fara yi maka gini kyauta. Amma maganar gaskiya ka sayar masa da filin ganin kana da wani wurin da za ka iya fara naka ginin na daban."

Fred Kaluwe Milanbo ya ce:

“Da sauki tunda wani ne ke gini a filinka. Da farko na zaci kudi ka dinga turawa ana yi maka ginin da ba ka so.”

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Memory Mwila ta ce:

“Ga yadda wannan mutum ya gina katon gidan nan, hakan ya na nuna ka dade ba ka je filin ba. Ka kyale shi ya ci gaba kawai.”

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164