Kotu ta bukaci Shehi a Dubai ya biya tsohuwar matarsa $734m da 'ya'yansu
- Kotu ta umarci Mohammed Bin Rashid Al Maktoum ya biya tsohuwar matarsa, Haya Bint al-Hussein da yaransa dala miliyan 734
- Alkalin kotun da ke London, Philip Moor ya bayar da umarnin inda ya ce Al Maktoum ya biya ta kudin cikin watanni uku saboda tsaro da batar sarkoki da suturunta
- A cewar alkalin, wajibi ne ya ci gaba da biyanta fan miliyan 11 duk shekara saboda makarantar yaransu wanda zai zama cikin fan miliyan 290 din
Dubai, UAE - Wata kotu a Ingila ta umarci Mohammed bin Rashid Al Maktoum, shugaban Dubai, ya biya tsohuwar matarsa, Haya Bint Al-Hussein dala miliyan 734 da yaranta.
Kamar yadda Aljazeera ta ruwaito, wannan ce mafi yawan dukiya da kotun Ingila ta taba ganin an yanka wa wani.
Philip Moor, wani alkalin London, ya umarci Al Maktoum da biyan tsohuwar matar tasa fan miliyan 251.5 cikin watanni uku don ta mayar da abubuwan ta kamar sarkoki da sutturunta.
Wajibi ne ya ci gaba da biyanta fan miliyan 11 duk shekara saboda kulawa da yaransu yayin da suke karatu ta yarjejeniyar banki na fan miliyan 290, kamar yadda yayi hukuncin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da sauran kudaden zasu zama na ilimi da sauran harkokin rayuwar yaransu, Premium Times ta ruwaito.
Wannan zai taimaka wa sarauniyar bayan rabuwar auren nasu kamar yadda Alkali Philip Moor ya yanke hukunci a ranar Talata.
Ya ce shugaban na Dubai, wanda bai bayyana wata shaida akan karar ba, ya nuna tsananin tsaro akan kansa bayan wani alkalin ya gano yadda ya umarci a kwace wayoyi da sauran dukiyoyinta.
Kudaden da Sheikh din zai biya ga iyalansa zai yawaita saboda yadda zai ware kudaden tsaro na duk shekara ga yaransa har bayan sun kammala karatunsu.
A wata takarda, Sheikh din ya ce yana iyakar kokarin ganin ya samar wa yaransa duk abinda su ke so.
Lauyoyin Haya sun musanta maganar nan da yayi.
Kotunan iyali na London sun yi fice akan kwatar wa mutane hakkinsu tare da yadda alkalai suke jajircewa wurin amsar dukiya mai tarin yawa ga mata idan aurensu ya mutu.
Kafin ranar Talata, wani sanannen alkali ya umarci biyan tsohuwar matar biloniya Farkhad Akhmedov fan miliyan 450, duk da dai daga baya sun zauna sannan su ka sulhunta akan zai biyata kasa da daya bisa ukun kudin.
A shekaru biyu da suka gabata, kotunan London sun dade suna yanke hukunce-hukunce wadanda su ke tayar da tarzoma ga gidajen sarautar Dubai.
Dama tun da aka fara shari’ar Ms Haya a tsare take don gudun abinda zai iya kaiwa ya komo.
Abinda kadai ta bukata shi ne kudin tsaron lafiyarta sai kuma na dukiyarta da tayi asara.
A cikin shari’ar, Alkali Moor ya bai wa iyalin fiye da fan miliyan biyar don shakatawa wanda zasu fita yawon bude ido cikin shekara daya a cikin jirgin sama na musamman.
An ware kusan fan 300,000 don kulawa da dawakin su da sauran kayan da suke kiwatawa.
Canada ta dage takunkumin hana shigar 'yan Najeriya kasar
A wani labari na daban, gwamnatin kasar Canada ta dage takunkumin da ta saka na haramta wa jama'ar kasashe goma na Afrika da suka hada da Najeriya shiga kasar.
TheCable ta ruwaito cewa, Jean-Yves Duclos, ministan lafiya na kasar Canada, ya sanar da wannan hukunci a wani jawabi da yayi wa manema labari a ranar Juma'a.
Wannan cigaban ya na zuwa ne bayan makonni uku da gwamnatin kasar Canada ta haramta wa kasashe goma da suka hada da Najeriya daga shiga kasar kan tsoron yada sabon nau'in cutar korona na Omicron.
Asali: Legit.ng