Sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron ya bulla kasar Saudiyya, Sun fara daukar matakai

Sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron ya bulla kasar Saudiyya, Sun fara daukar matakai

  • Kasar Saudiyya ta sanar da cewa sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron ya bulla a kasar
  • Hukumomi sun tabbatar da gano cutar a jikin wani ɗan kasar da ya yi tafiya zuwa wata ƙasa a arewacin Afirka, amma ba su bayyana sunan kasar ba
  • A halin yanzun Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgan jiragen sama daga wasu kasashen nahiyar Afirka 14

Saudi Arabia - Ƙasar Saudi Arabia ta tabbatar da bullar sabon nau'in cutar COVID19 dake jan hankalin duniya a yanzun mai suna Omicron.

BBC Hausa ta rahoto ma'aikatar lafiya ta ƙasar na cewa cutar ta shiga Saudiyya ne daga wata kasa dake arewacin Afirka.

Kamfanin Dillancin labarai na ƙasar ta Saudiyya, (SPA) yace tuni mahukunta suka killace wanda aka gano sabon nau'in cutar a jikinsa da kuma dukkan mutanen da ya yi mu'amala da su.

Kara karanta wannan

Omicron: Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 da ke neman sake rufe kasashe

Sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron ya bulla kasar Saudiyya, Sun fara daukar matakai
Sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron ya bulla kasar Saudiyya, Sun fara daukar matakai Hoto: BBC Hausa
Asali: Facebook

A cewar mahukunta mai ɗauke da cutar ɗan asalin Saudiyya ne da ya yi tafiya zuwa wata ƙasa a Afirka, sai dai ba su bayyana sunan ƙasar ba.

Saudiyya ta hana kasashen Afirka 14 shiga kasar

Masarautar saudiyya ta sanar da dakatar da shige da ficen mutane daga kasashen Afirka 7 saboda barkewar sabon nau'in COVID19.

Ƙasashen da lamarin ya shafa sun haɗa da Malawi, Zambia, Madagascar, Angola, Seychelles, Mauritius da kuma Comoros.

Tun a ranar Jumu'a, ƙasar ta sanar da hana zirga-zirgan jiragen sama masu shiga da fita daga ƙasashen South Africa, Namibia, Botswana, Zimbabwe, Mozambique, Lesotho, da Eswatini.

Jaridar Arab News ta rahoto cewa hakan yasa adadin kasashen da dokar hana shiga da fita ya shafa a nahiyar Afirka yakai 14.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: NCDC ta tabbatar da ɓullar nau'in cutar korona na Omicron a Najeriya

Hakanan kuma duk wanda ya kasance a ɗaya daga cikin waɗan nan kasashe kwanaki 14 da suka wuce kafin isowarsa ba zai samu damar shiga Saudiyya ba.

Yan kasa da yan waje da aka baiwa damar shiga zasu killace kansu na tsawon kwana 5, ko da kuwa sun yi rigakafin cutar.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta yi kira ga mutanen da suka shigo ƙasar daga waɗan nan kasashe bayan 1 ga watan Nuwamba, su yi gwajin cutar.

A wani labarin na daban kuma Gwamnatin taraya ta cika alkawarinta na hana wadanda basu yi rigakafn Korona shiga ofisoshinsu

Jami'an tsaro sun hana ma'aikatan gwamnatin da ba suyi rigakafin Korona ba shiga ofishoshinsu a sakatariyar gwamnati dake birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta yi kira ga Gwamnati ta dage wannan doka zuwa watan Maris 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262