Yanzu nan: Jirgin Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron zaman lafiya na Duniya

Yanzu nan: Jirgin Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron zaman lafiya na Duniya

  • Dazu nan Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin birnin Faris domin halartar taron PPF da za ayi.
  • Shugaban Najeriyar zai yi zama da Emmanuel Macron, kuma zai zauna ne a fadar Palais de l’Élysée.
  • Bayan ganawarsa da shugaba Macron, Buhari zai yi jawabi a gaban shugabannin Duniya a PPF.

Paris - A ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hallara babban birnin kasar Faransa watau Faris.

Mai girma Muhammadu Buhari zai zauna a fadar shugaban kasa na Palais de l’Élysée na kwana daya a matsayin babban bakon Emmanuel Macron.

Mai magana da bakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana wannan dazu. Adesina yace jirgin shugaban kasar ya sauka da karfe 2:45 na rana.

Buhari da Macron za su tattauna a kan abubuwan da suka shafi Najeriya da kasar Faransa, musamman tattalin arziki, ilmi, kiwon lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Dole kirista ne zai gaji Buhari, In ji Ƙungiyar Kirista ta PFN

Buhari zai halarci taron PPF na bana

Bayan ya gana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, Buhari zai halarci taron Faris na zaman lafiya (PPF), wanda za a shafe har kwanaki uku ana yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jirgin Buhari
Buhari a kasar Faransa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Punch tace daga ranar Alhamis, Buhari zai hadu ne da shugabannin kasashe da kungiyoyin duniya da ‘yan kasuwa a Grande Halle de La Villette.

Jaridar The Guardian tace shugabannin za su tattauna a kan yadda za a kawo zaman lafiya a Duniya.

Buhari zai yi jawabi a gaban manyan Duniya

A jawabinsa, Buhari zai yi wa shugabannin bayanin irin halin da Najeriya ta ke ciki, da kokarin da gwamnatinsa take yi na ganin an samu zaman lafiya.

Sauran wadanda za su yi jawabi a taron sun hada da Macron, Kamala Harris ta kasar Amurka, da kuma Firayim Ministan Bangladesh, Sheikh Hasina.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

A taron wannan shekarar, shugabannin Duniyar za su waiwayi wasu ayyuka 80 da ake yi a kasashe dabam-dabam domin magance matsalolin tsaro.

Muhammadu Sanusi ya na rubuta littafi

Dazu nan ku ka ji cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya na rubuta littafin da zai yi tonon silili a kan yadda aka yake shi da yake gwamnan bankin CBN.

Tsohon Sarkin na Kano da gwamnan na CBN yace an yi ta huro wuta domin a hana kawo tsarin bankin musulunci, har aka bada shawarar ayi waje da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel