Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

  • Tashin hankali da tsoro sun fada zukatan jama'ar kasar Sudan da ke Afrika kan wani lamari mai kama da juyin mulki
  • Manyan jaridun duniya sun ruwaito cewa, a ranar Litinin, 25 ga Oktoba, sojoji sun damke shugaba Abdallah Hamdok
  • Hakazalika, sojojin sun hada da wasu jiga-jigan gwamnatinsa da ministocinsa yayin da suka rufe titunan da ke kaiwa fadar shugaban kasan

Sudan - Rahotanni masu girgiza zukatan da ke zuwa a halin yanzu shi ne na daurin talalan da sojojin kasar Sudan suka yi wa Firayin Ministan Abdallah Hamdok.

Kamar yadda Al-Jazeera ta wallafa, sojojin sun yi ram da Hamdok tare da wasu daga cikin ministocinsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kai sabon hari Yobe, sun sha ruwan wuta a hannun sojojin Najeriya

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa
Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa. Hoto daga Abdallah Hamdok
Asali: Facebook

Daga cikin jami'an gwamnatin Sudan da sojoji suka kama, akwai ministan masana'antu, Ibrahim Al-Sheikh, ministan yada labarai, Hamza Baloul da kuma mai bai wa Hamdok shawara kan yada labarai, faisal Mohammed Saleh.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda aka kama sun hada da mai magana da yawun majalisar zartarwa ta kasa, Mohammed al-Fiky Suliman da Ayman Khalid, gwamnan Khartoum.

An tattaro cewa, yayin da aka datse hanyoyin sadarwa, sojojin sun tsare tare da toshe dukkan tituna da gadojin da ke kaiwa zuwa babbar birnin Khartoum.

Cameroun Hudson, babban mabiyi a cibiyar zartarwar Afrika ta Atlantic ya cewa muryar Amurka: "Wannan babban koma baya ne ga damokaradiyyar Sudan."

Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu

A wani labari na daban, gwamatin Najeriya ta fada wa sojojin Mali su yi maza su saki shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, an soki tsare shugabannin da aka yi.

Jawabin ya ke cewa: “Gwamnatin tarayya ta na matukar tir da cigaba da tsare shugaban rikon kwarya, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane."
Mista Ferdinand Nwonye ya ce: “Wannan danyen aiki abin Allah wadai ne, kuma zai dawo da hannun agogo baya wajen dawo da mulkin Farar hula a Mali.”

Ma’aikatar harkar kasar wajen ta ce matakin da sojojin suka dauka barazana ne ga zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng