Mace mafi tsawo a duniya: Rumeyasa Gelgi 'yar ƙasar Turkiyya

Mace mafi tsawo a duniya: Rumeyasa Gelgi 'yar ƙasar Turkiyya

  • Rumeysa Gelgi daga Turkiyya ce mace mafi tsawo a duniya a halin yanzu a cewar na Guiness World Records
  • Gelgi tana fama da wani cuta da ake kira Weaver syndrome wadda ke saka kasusuwan mutum suyi tsawo fiye da na sauran mutane
  • Wani abin mamaki shine a halin yanzu na miji wanda ya fi tsawo a duniya shima dan kasar Turkiya ne mai suna Sultan Kosen

Kundin tarihi na Guiness World Records ya tabbatar da cewa wata mata mai shekaru 24 'yar kasar Turkiyya ne mace mafi tsawo a duniya a halin yanzu.

A cewar Guiness World Records, Rumeysa Gelgi ta lashe kambun ne da tsawon 215.16cm (7ft 07in) kamar yadda ya zo a ruwayar BBC Pidgin.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Mace mafi tsawo a duniya: Rumeyasa Gelgi 'yar ƙasar Turkiyya
Rumeyasa Gelgi 'yar ƙasar Turkiyya, mace mafi tsawo a duniya. Hoto: Guiness World Records
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sake gwada tsawon Rumeysa a wannan shekarar, bayan an fara bata kambun mace yar kasa da shekara 19 a 2014, a lokacin da ta kai shekaru 18, tsawonta ya kai 215.16cm (7ft 0.7in) a lokacin.

Rumeysa ta ce tsawonta ya kan saka mutane mamaki idan tana tafiya a cikin gari, amma mafi yawancin mutane su kan fada mata kalamai na kara kwarin gwiwa a haduwarsu na farko.

Weaver syndrome: Sanadin tsawonta?

Wani cuta da ake kira Weaver syndrome ne ya yi sanadin tsawon da Rumeysa ke da shi fiye da na sauran mutane, cutar ya kan saka kasusuwan mutum su rika girma sosai da ma wasu abubuwan.

Sakamakon wannan cutar da ta ke fama da shi, Rumeysa na amfani da kujerar guragu ne mafi yawancin lokaci amma ta kan iya tashi ta yi tafiya na kankanin lokaci da taimakon abin tafiya.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Tun da aka kafa bata kambun mafi tsawon a 2014, Rumeysa ta ce ta yanke shawarar cewa ya kamata ta yi amfani da damar da ta samu domin wayar da kan mutane kan irin cutar da ta ke fama da shi.

Wani abin mamaki game da kambun shine Rumeysa yar Turkiya da Sultan Kosen (251 cm; 8 ft 2.8 in) shima dan Turkiyya ne mace da namiji mafi tsawo a duniya a halin yanzu.

Tsohon wanda ke rike da kambun shine Yao Defen dan kasar China mai tsawon 233.3 cm (7 ft 7 in) a gwajin da aka masa na karshe a 2010.

Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

A wani rahoton, wasu masoya, Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.

Kara karanta wannan

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164