Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan

Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan

  • Mako daya bayan harin Bam da ya hallaka mutum 100 a Kunduz, an sake kai harin Bam Afghanistan
  • Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa mutane da dama sun mutu
  • Jami'an tsaron Taliban sun isa wajen domin bincike

Kandahar - Akalla mutum 32 sun rasa rayukansu yayinda 45 sun jigata sakamakon harin bam da aka kai asibitin shi'a dake birnin Kandahar dake kudancin Afghanistan, jami'an lafiyan kasar sun bayyana.

Wannan hari ya auku ne yau Juma'a, 15 ga Oktoba a Masallacin Bibi Fatima, Masallacin Shi'a mafi girma a birnin, Aljazeera ta ruwaito.

Kakakin Ministan harkokin cikin gida, Qari Sayed Khosti, ya sanar da faruwan hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace:

"Muna alhinin samun labarin Bam da ya tashi a Masallacin yan uwa Shi'a a birnin Kandahar inda adadin mutanenmu sukayi shahada kuma wasu suka jikkata."

Kara karanta wannan

Tsoho dan shekara 71 ya mutu yayin Jima'i da yarinya yar gidan magajiya a Shagamu

"Jami'an tsaron Taliban sun isa wajen domin ganin abinda ya auku da kuma damke wadanda suka aikata."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan
Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan
Asali: Original

Wani mai idon shaida ya bayyana AFP cewa yaji tashin Bam har uku, daya a wajen kofar Masallaci, daya a kudancin Masallaci da kuma daya a wajen alwala.

Aljazeera ta bayyana cewa majiyoyi sun bayyana mata gawawwaki sun cika wajen .

Har yanzu dai babu wanda yayi ikirarin aikata wannan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng