Sharif Lawal
6206 articles published since 17 Fab 2023
6206 articles published since 17 Fab 2023
Tantirin shugaban 'yan bindiga, Dogo Gide, ya fafata da mayakan Boko Haram da ke biyayya ga Sadiku. Fadan da aka gwabza ya yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sojoji da su shiga cikin dazuzzuka domin fatattakar 'yan bindigan da suke boye a ciki.
Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Neja. Mutane da dama an kwantar da su a a asibiti. Hukumomi sun yi bayani kan cutar wacce take sanya mutane sumewa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnatin Katsina ta goyi bayan shirin da ta bullo da shi na yin sulhu da 'yan bindiga domin kawo karshen rashin tsaro.
Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a hare-haren da suka kai a sansaninsu.
Wani babban jigo a jam'iyyar APC a jihar Yobe, Sa'idu Hassan Jakusko, ya sanar da ficewarsa daga APC. Ya nuna cewa ba a saka musu ba duk da wahalar da suka yi.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan ta'addan ISWAP suka yi yunkurin kai wa a jihar Yobe.
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, ta bukaci mutanen Gabashin jihar da su sanya ido kan 'yan ta'addan da ke tserewa sojoji.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), sun samu nasara kan wasu mutane biyu da ake zargi. Kafin cafke su sai da aka ba hammata iska.
Sharif Lawal
Samu kari