Sharif Lawal
4005 articles published since 17 Fab 2023
4005 articles published since 17 Fab 2023
Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya koka kan matsalar cin hanci da rashawa. Ya ce cin hanci da rashawa ya hana a samu ci gaba a kasar nan.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da yi wa likitoci karin albashi a jihar. Gwamna Zulum ya amince a rika biyansu daidai da na tarayya.
Jigo a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci kungiyar ACF da ta daina sukar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin Arewacin Najeriya.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa. Daga cikin 'yan ta'addan da aka kashe akwai kwamandansu Munzur Ya Audu.
Wasu 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan wani matashin lauya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun bi matashin lauyan har gida sannan suka bude masa wuta.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa baya tsoron binciken da hukumar EFCC ke yi masa. Ya nuna cewa a shirye yake ya kare kansa.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi alhinin rasuwar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi. Marigayin ya rasu yana da shekara 93 a duniya.
An samu kuskuren rashin fahimta tsakanin jami'an tsaro na 'yan sanda da 'yan banga a jihar Anambra. Jami'an tsaron sun bude wuta ga junansu a cikin dare.
Hakimin garin Kurfi da ke jihar Katsina, Alhaji Ahmadu Kurfi, ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin shi ne tsohon shugaban hukumar FEDECO ya rasu yana da shekara 93.
Sharif Lawal
Samu kari