Aiki zai dawo baya, APC ta ce ba ta shirya gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya ba

Aiki zai dawo baya, APC ta ce ba ta shirya gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya ba

- APC ta karyata jita-jitar cewa za a fara shirin gudanar da zaben Shugabanninta

- Jam’iyyar tace yanzu ta dawo daga hutun sallah, ba a karkare shirye-shirye ba

- John James Akpanudoedehe ya bada sanarwar nan a madadin kwamitin riko

Kwamitin rikon kwarya da za su shirya gangami da taron shugabannin jam’iyyar APC ya ce bai shirya gudanar da zaben sababbin shugabanni ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto kwamitin Mai Mala Buni ya na cewa ba su shirya gudanar da zabe ba, kamar yadda wasu suke yadawa a kafafen labarai.

Rahoton ya ce hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran jadawalin zaben shugabannin jam’iyyar APC da za ayi zai fito a cikin makon nan.

KU KARANTA: Ban da burin takara - Osinbajo

Sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC mai mulki, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar da jawabi, ya musanya rade-radin da ke ta yawo.

Sanata John James Akpanudoedehe yake cewa masu yada jita-jitar za a fito da jadawalin zaben shugabanni, wasu ne da ke fake wa da sunan jam’iyya.

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi kira ga jama’a su yi watsi da labaran bogin da ke yawo, ta ce aikin wasu ‘yan taki zama ne, da nufin kawo rikici cikin APC.

“Hankalinmu ya zo ga wasu tulin labarin bogi da ake faman kitsawa a wasu sassan yada labarai game da shirin gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC.”

KU KARANTA: Matan Kudu suna so Gwamnan Kogi ya yi takarar Shugaban kasa

Aiki zai dawo baya, APC ta ce ba ta shirya gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya ba
Taron APC NEC Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

“Bamu taba yin karya game da ayyukan jam’iyyarmu ba, kuma babu dalilin yin haka.” Inji Akpanudoedehe.

Jawabin John James Akpanudoedehe ya ce kwamitin rikon kwaryan CECPC na gwamna Mai Mala Buni ya gyara yadda jam’iyya ta ke gudanar da al’amuranta.

“A ranar Litinin, 17 gaa watan Mayu, 2021, aka dawo aiki a sakatariyar jam’iyyar APC, kuma za a cigaba da aiki a kan muhimman ayyukan da ke gaban jam’iyya.”

Kamar yadda aka saba, APC ta ce sa ta sanar da lokacin da za a yi zabe, zuwa yanzu ba a sa rana ba.

A jiya an ji cewa Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce nan da wata daya rak za a buga gangar siyasar 2023 a jihar Delta, har ya fara maganar wanda zai zama magajinsa.

Ifeanyi Okowa ya ce a cikin watan Yuni zai fadi wanda zai zama sabon Gwamnan jihar Delta. Amma gwamnan mai-ci ya bada wasu sharudan da magajinsa zai cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng