Direban Shugaba Buhari ya dawo da kudi a Saudiya
Wani mai amfani da shafin zumunta na Facebook, Buhari Sallau ya rubuta labarin yadda direban Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sa’idu Afaka, ya rike gaskiya har kasar Saudiya.
A cewar rahoton, ya tsinci wani jaka dake dauke da makudan kudin kasar waje, wanda wani ya batar ya kuma kaima hukumar da ta dace. Karanta yadda majiyar ta ruwaito a kasa…
KU KARANTA KUMA: Tattalin arzikin Najeriya zai inganta- Buhari
“DIREBAN SHUGABA BUHARI YA TSINCI KUDI DA AKA BATAR A KASAR SAUDIYA YA KUMA MAYAR DA KUDIN GA HUKUMA!
Abun farin ciki, Ina alfaharin rahoto maku cewa ma’aikaci Sajen Sa’idu Afaka direban shugaba Buhari wanda ke aikin hajji a birnin Macca, kasar Saudiya ya tsinci wani jaka dake dauke da makudan kudin kasar waje wanda suka hada da Dlar Amurka da kudin Sudiya Riyal na wani da ya bata. A lokacin da Afaka ya gane cewa kudi ya tsinta, ya nemi hukuma cikin gaggawa ya mika su ga kwamandan aikin hajji dake Ummul Jud a garin Macca, ya kuma nemi da su nemi mammalakin jakar. A lokacin da ya kai gudin ga hukuma ne suka lura cewan akwai Faspo din mai jakar a cikin kudin.
Hmmmmmm babu shakka hakan da ya yi yayi kyau sosai!
Asali: Legit.ng