Matukin jirgin shugaba buhari, kyaftin Chinyelu
Kyaftin Chinyelu Chizoba Ndibuisi matukin jirgin saman Shugaban kasa ne kuma yana tuka jirgin saman Najeriya mai lamba 001.
Ya taba aiki a matsayin matukin jirgin Air Peace. Matukin jirgin shugaban kasa na son shakatawa da kwantar da hankalinsa ta hanyar wasan da ya fi so, wasan kwallon kan tebur wato tennis. A yanzu haka yana kasar Amurka tare da uban gidansa, Shugabna kasa Muhammadu Buhari, wanda ya halarci taron majalisar dinkin duniya zama na 71 a birnin New York dake kasar Amurka.
KU KARANTA KUMA: Mulkin Arewa a kasar Najeria tun 1960
Kalli hotunan Kyaftin Chiyelu a kasa:
A ranar Asabar 17 ga watan Satumba, Kaftin Chinyelu ya tuka Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka tashi daga kasar Najeriya domin shugaban kasa ya halarci taron majalisar dinkin duniya (UN) a kasar Amurka. Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kuma halarci wani gamuwa tare da shugaban kasar Amurka, Barack Obama a ranara Talata, 20 ga watan Satumba, inda shugabanni guda biyun zasu tattauna kan al’amarin “goyon bayan da kasar Amurka zata ci gaba da bayarwa kan tsaro da canjin tattalin arziki a kasar, haka kuma da kokarin da gwamnati keyi kan kungiyar yan ta’addan Boko Haram.
Asali: Legit.ng