Gwamnan jihar Bauchi ya ziyarci shugaba Buhari

Gwamnan jihar Bauchi ya ziyarci shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar a fadar sa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar 31 ga watan Augusta.

Gwamnan jihar Bauchi ya ziyarci shugaba Buhari
Buhari da Abubakar

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkan kafafen watsa labarai Femi Adesina ne ya watsa hotunan ganawar shugaban da gwamnan a shafinsa na Facebook.

Kazalika gwaman jihar Kogi Yahaya Bello ya kai ma shugaban kasa ziyara a ranar alhamis 25 ga watan agusta.

A kwanakwanan nan ma dai Alaafin of Oyo, Sarki Lamidi Adeyemi III ya gana da shugaba Buhari a fadarsa dangane da matsalar tsaro da kasa ke fama da ita. Sarkin bayyana cewa Shugaba Buhari ya bukaci sarakunan gargajiya dasu rubuto korafin su dangane da tafiyar da gwamnatin sa.

Yace wanda “a matsayina na daya daga cikin manyan sarakunan kasar nan, na tura mai da takardan korafi a baya, dalilin da yasa kenan ya gayyace ni in zo inyi mai karin bayani dangane da batutuwan da na mika mai.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel