Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai da sukayi fice daga jaridun najeriya a yan Juma’a 12 ga watan Augusta.

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya nace a jiya cewa aragizon kasafin kudi ba laifi bane, cewa babu dan majalisan da za’a iya bincike a kai. Ya fada haka ne a babban birnin tarayya Abuja.

Har ila yau jaridar the Nation ta ci gaba da cewa daya daga cikin dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP, Cif Raymond Dokpesi ya bayyana cewa jam’iyyar zata rabu idan gwamnoni suka gabatar da sabon shugaba a jam’iyyar. Ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis 11 ga watan Augusta.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, mambobin kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) sun nuna jin dadinsu a garin Onitsha ,yayinda gwamnatin tarayya  ta hannun lauyan lauyoyi kuma Ministan Shari’a, Ibrahim Malami ya bada da umarnin sakin yan kungiyar da hukumomin tsaro daban-daban suka kama a lokacin wani taron addu’a a watan Fabrairu, Aba, dake jihar Abia.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Shettima ya kaddamar da kungiyar addini a jihar Borno

Bisa ga jaridar Punch, Hukumar yan sandan jihar Ogun sun kama wani dan kasuwa mai shekaru 32, Ezekiel Igbokwe, kan zargin cewa ya kashe saurayin matarsa  mai suna Victor Olatundun.

An ruwaito cewa Igbokwe ya kashe Olatundun bayan ya kama shi yana jima’I da matarsa a gidan auransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng