Gwamna Shettima ya kaddamar da kungiyar addini a jihar Borno

Gwamna Shettima ya kaddamar da kungiyar addini a jihar Borno

-Gwamna Shettima ya kaddamar da zasu lura da wa’azi a jihar Borno

-Yace wannan zai dakatar da sabonta kungiyar Boko Haram

-Wannan yayi kama da dokar jihar Kaduna wanda suke duba ayyukan addini

Gwamnan jihar Borno Kasim Shettima ya bi sahun takwaransa, Nasir El-Rufai, ta hanyar kaddamar da wani hukuma da zata tafiyar da wa’azin muslunci a jihar Borno.

Yunkurin Gwamnan jihar Kaduna El-Rufa’I na kafa hukumar da zata lura da yanayin wa’azi bai tsaya a jihar sa kawai ba saboda takwaransa gwamnan jihar Borno ya bi sahunsa koda dai nasa ya tsaya a kan masu wa’azin musulunci ne kawai.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar, musulunci na jihar Borno wato , Borno State Islamic Preaching Board, (BSIPB) zata dunga lura da masu wa’azi wadanda zasu so baza koyarwan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Dogara yayi watsi da gayyatar Yan sanda

Shettima yace akwai wani shiri da ake yi na kafa kungiyar da zasu  dunga lura da makaratun Islamiyya, Tsangaya ko Almajiri da makarantun larabci domin kare makarantun daga wasu da muke da muggan nufi.

Babban limami Zannah Ahmed ne zai jagoranci hukumar tare da wasu da zasu wakilci sauran guraren musulunci.

Shettima yayi Magana kan yawan yan Boko Haram a jihar da kuma dalilin da zai sa yan kungiyar su dage gurin hana yada ta’addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng