Dan wasa Cristiano Ronaldo na daf da shirin dawowa filin wasa

Dan wasa Cristiano Ronaldo na daf da shirin dawowa filin wasa

– Babban dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya dawo fili.

– Dan wasa Cristiano Ronaldo ya samu rauni ne a wasan karshe na Gasar UEFA EURO 2016.

– Dan wasan bayan Kungiyar, Pepe ma ya dawo.

Dan wasa Cristiano Ronaldo na daf da shirin dawowa filin wasa

 

 

 

 

 

 

 

 

Idan ba a manta ba, dan wasa Cristiano Ronaldo ya samu rauni a gwiwar sa a wasan karshe na Gasar UEFA EURO 2016, dan wasan yayi karo ne da Dmitiri Payet na Kasar Faransa lokacin da suka fafata a wasan na finals, watau wasan karshe, wanda kuma Kasar Portugal din ta dauka a Kasar Faransa. Dan wasan na duniya bai samu buga wasan UEFA SUPER CUP da Kungiyar ta sa ta Real Madrid ta buga da Sevilla ba a ranar Talatan nan. Duk da dai babban dan wasan bai samu bugawa ba, Real Madrid din ta doke Sevilla da ci 3-2 bayan an kai ga Karin lokaci.

KU KARANTA: REAL MADRID TA DAUKI UEFA SUPER CUP

Bayan ya samu sauki, Ronaldo ya sanar da magoya bayan sa a shafin san a Instagram fa cewa, ya samu lafiya. @Cristiano Ronaldo ya rubuta: “Ina mika godiya ga dukkanin magoya baya na. Ina kuma sanar da su cewa yanzu komai lafiya lau. Ina nan zan dawo da karfi na kwanan nan. Nagode! Ubangiji kuma ya taimaki Kasar mu ta Portugal.”

Dan wasan dai ya fara atisaye da Kungiyar, haka ma kuma dan wasan bayan nan kuma dan Kasar Portugal din, Pepe ya dawo. Pepe ya dawo ne a ranar Laraba, inda suka yi atisaye tare ds Cristiano. Sauran yan kungiyar za su huta na kwana guda saboda wasan da suka buga na UEFA SUPER CUP ranar Talata, sai zuwa ranar Alhamis kowa zai dawo aiki.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng