Abun al'ajabi: Kalli hotunan tsohuwa mai shekaru 59 da ciki

Abun al'ajabi: Kalli hotunan tsohuwa mai shekaru 59 da ciki

Akwai wasu labarai da zasu zama ishara kuma su baku karfin gwiwar ci gaba da rayuwa. Lalle ne idan da rai da rabo.

Mutane da dama sun fuskanci wahala iri-iri a gidan Auransu saboda al’amuran da suka shafi rashin haihuwa. Wasu ma’auratan ma sun rabu saboda rikicin dake afkuwa a duk lokacin da sukayi Magana a kan rashin haihuwa. Muna jin dadi idan muka samu labarin samun dacewa ko nasara ga ma’auratan da suka fuskanci kalubale kan wannan lamari na rashin haihuwa.

Kira shi duk abunda ka so, abubuwa na faruwa a duniya kuma bazamu ki yin Magana akan suba. Abubuwan al’ajabi na ci gaba da faruwa, kuma mutane na nuna godiyarsu ga ni’imar Ubangiji da jin kan sa.

KU KARANTA KUMA: An kama wani mutumi yana kokarin cire kan abokinsa

Babu tantama Labarin Claudette Cook zai zama ishara a gareka, labarin mai cikin yar shekaru 59 tabbaci ne ke nuni ga Allah mai daukakane. Tayi aure da mijinta na tsawon shekaru tara; likita ya fada mata cewa bazata taba haihuwa ba. Cook ma tana tantamar zama uwa saboda shekarunta.

Abun al'ajabi: Kalli hotunan tsohuwa mai shekaru 59 da ciki

Duk da gazawar shekarunta yanzu gata tana fama da cikin tagwaye. Zata haifi yara maza kamar yanda Allah ya tsara canja tunaninta ya kuma bata sahidar cewa shi mai iko ne.

Abun al'ajabi: Kalli hotunan tsohuwa mai shekaru 59 da ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel