Da duminsa: Majalisa ta amince da kato bayan kato kadai a zabukan fidda gwanin jam'iyyu

Da duminsa: Majalisa ta amince da kato bayan kato kadai a zabukan fidda gwanin jam'iyyu

  • Majalisar dattawan kasar nan ta aminta da dokar zabe wacce ta ce zaben kato bayan kato kadai za a dinga a zabukan fitar da gwani
  • Kamar yadda majalisar ta amince da bukatar da Sanata Yahaya Abdullahi ya mika, ta ce wannan zaben fitar da gwanin kadai ta aminta da shi
  • Da farko dai dokar majalisar kan zabukan fitar da gwani ta amince da zaben kato bayan kato ko ta wakilan jam'iyyar siyasa kadai

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta aminta da gyaran dokar zabe wacce ta amince wa jam'iyyun siyasa da su koma zabukan fitar da gwanaye ta hanyar zabukan kato bayan kato.

The Nation ta ruwaito cewa, majalisar tun farko ta amince da dokar zaben da ta amince wa jam'iyyun siyasa su yi zaben kato bayan kato ko kuma zaben fitar da gwani ta hanyan amfani da wakilan jam'iyya.

Read also

Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

Da duminsa: Majalisa ta amince da kato bayan kato kadai a zabukan fidda gwanin jam'iyyu
Da duminsa: Majalisa ta amince da kato bayan kato kadai a zabukan fidda gwanin jam'iyyu. Hoto daga thenationonlineng.net
Source: UGC

Wannan hukuncin ya biyo bayan majalisar dattawan da ta karba wata bukata wacce Sanata Yahaya Abdullahi daga Kebbi ta arewa ya mika gaban majalisar.

Karin bayani na nan tafe...

Source: Legit Nigeria

Online view pixel