Yadda tsofaffin Gwamnoni, Sanatoci da wasu ‘Yan Najeriya suka dankare Biliyoyi a waje
- Masu kudin Najeriya suna tara kadarori da dukiyoyi a bankunan kasar waje
- Bincike ya nuna ana juya arzikin a boye, don haka sam ba a cire masu haraji
- Akwai wasu ‘Yan Najeriya da sunayensu ya fito a badakalar Pandora Papers
Nigeria - Najeriya na cikin kasashen da ake fama da matsanancin fatara a Duniya. Alkaluma sun nuna 90% na al’ummar wasu jihohi ba su samun ko da $1 a rana.
Amma duk da haka, akwai tsirarru da suka mallaki biliyoyin kudi, wasu ta hanyoyin da ba su dace ba.
Jaridar Premium Times tace bayanan da aka samu daga fallasar Pandora Papers sun nuna akwai wasu manya da suka boye dukiyoyi masu yawa a kasashen waje.
Cikin wadannan mutane su 21 da suke kasuwanci a ketare, akwai wanda yana da Dala miliyan 10, sannan ya na da kadarorin fam miliyan £77.3 a Amurka da Ingila.
Wanda ya mallaki wannan tulin dukiya ya ajiye su ne a bankin Standard Chartered a Guernsey, Ingila.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akwai wasu mutane biyu da suka mallaki kadarorin $511,860 da fam £50,000 a bankin Standard Bank a birnin Jersey. Wannan dukiya ya kusa Naira miliyan 250.
Rahoton yace a yadda farashin canji yake yau a CBN, adadin dukiyar da ake magana ya kai Naira biliyan 84. Ana canjin Dala a babban bankin kasar a kan N410-N411.
A kasuswar canji, ana saida Dalar Amurka a kan N558, yayin da Pounds Sterling ya kai N775.
Pandora Papers ya fallasa wasu manya
Binciken da aka yi ya nuna cewa shugabanni da jami’an gwamnati da attajirai da-dama daga kasashe akalla 91 sun tara tulin dukiyoyin da suke juya wa a boye.
Daga cikin wadanda aka samu a Najeriya akwai tsofaffin gwamnonin mulkin soja, tsohon soja, hadimin tsohon shugaban kasa da wasu ‘yan kasuwa da attajirai.
Rahoton da aka fitar a ranar Litinin bai iya bada sunayen mutanen da asirin na su ya tonu ba.
A jiya aka ji Yemi Osinbajo ya soki tsare-tsaren CBN, mataimakin shugaban kasa ya bada shawarar yadda za a rika samun Dala, kuma a bunkasa tattalin kasar.
Farfesa Osibajo ya fada wa Godwin Emefiele cewa akwai gyara a lamarin bankin CBN. Osinbajo ya bayyana hakan ne a wajen bitar da aka shirya wa Ministocin tarayya.
Asali: Legit.ng