Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da Gwamna Obaseki a fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da Gwamna Obaseki a fadar shugaban kasa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
  • Sun yi ganawar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Laraba, 13 ga watan Oktoba
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana hakan, sai dai bai bayar da cikakken bayani kan ganawar tasu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba.

mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Mista Femi Adesina ne ya bayyana hakan yayin da ya wallafa hotunan ganawar tasu a shafinsa na Facebook.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da Gwamna Obaseki a fadar shugaban kasa
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da Gwamna Obaseki a fadar shugaban kasa Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Sai dai bai bayar da cikakke bayani kan abun da ganawar tasu ta kunsa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Read also

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a gidan gwamnati a ranar 13 ga Oktoba 2021."

Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

A wani labarin, mun kawo a baya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.

Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya gana da Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel