Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun sace limamin cocin katolika
- Babban limamin cocin katolika na St Theresa da ke Umuahia, jihar Abia, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane
- An gano cewa miyagun sun tare shi a babbar hanyan Enyiukwu inda suka fito da shi daga motarsa kirar Toyota Corolla
- A safiyar Laraba ne suka tirsasa shi domin shiga motar jif din su wacce daga bisani suka bata wuta tare da tserewa
Umuahia, Abia - Rabaren Fada Godfrey Mark Chimezie na cocin Katolikan St Theresa da ke garin Umuahia a jihar Abia ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.
An sace sa a kan babbar hanyar Enyiukwu, yankin Ohokobe Afaraukwu da ke Ibeku a karamar hukumar Umuahia ta arewa a jihar, Daily Trust ta wallafa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu ganau sun ce masu garkuwa da mutanen sun tsare limamin cocin ne bayan kammala karatun safe da ya yi a St Gabriel da ke Okpururie, Afaraukwu.
Sun tirsasa shi ya fito daga motarsa kirar Toyota Corolla kuma suka saka shi a jif din su tare da yin gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Chimexie dan asalin jihar Enugu ne kuma an nada shi a matsayin babban shugaban cocin a farkon wannan shekarar.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng