Gwamnatin Buhari na shirin ba tsohon kamfanin Atiku kwangila mai tsoka ta bayan-fage

Gwamnatin Buhari na shirin ba tsohon kamfanin Atiku kwangila mai tsoka ta bayan-fage

  • Bincike ya nuna ana shirin a maida wa INTELS kwangilar tsaron jiragen ruwa
  • A 2019 ne NPA ta karbe kwangilar gadin da aka ba kamfanin a tashoshin ruwa
  • Alamu na nuna Minista ya dawo da INTELS cikin lissafi duk da bai cancanta ba

Abuja - Gwamnatin tarayya ta na sake shirin ba kamfanin INTELS kwangilar shekaru 25 domin su rika sa ido a kan jiragen ruwa a tashoshin Najeriya.

Wani bincike na musamman da Daily Trust ta yi, ya nuna kokarin ba wannan kamfanin kwangilar duk da cewa an yi waje da shi tun wajen neman kwangilar.

A lokacin da za a bada kwangilar tsaron jirage a 2019, shugabar NPA ta lokacin, Hadiza Bala Usman ta rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, tayi karar INTEL.

Usman tace kamfanin ya saba ka’idar da aka yi da shi, don haka aka cire shi a cikin masu neman kwangilar. Hakan ya sa kamfanin ya shigar da kara a kotu.

Kara karanta wannan

Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 a kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

Sauran kamfanonin da aka zaba cikin sama da 30 su yi takarar neman wannan kwangila ta biliyoyi sune; Pacific Silverline Ltd, da Isasha Investment Ltd.

Sai kuma kamfanonin ICA Logistics Ltd da wani Nexttee Oil & Gas Trading Company Ltd.

Hon. Rotimi Amaechi
Ministan sufuri, Hon. Rotimi Amaechi Hoto: www.encomium.ng
Asali: UGC

Gwamnati ta dawo da magana baya

Jaridar tace sai kwatsam aka ji ma’aikatar sufuri ta umarci hukumar NPA ta dawo da yarjejeniyar da ke tsakanin ta da kamfanin Intel bayan abin da ya faru.

NPA ta bi umarnin ma’aikatar tarayyar, ta kuma fara shirin yi wa wa’adin yarjejeniyar kwaskwarima zuwa tsakanin shekara 10-15, maimakon 25.

Har ila yau, NPA tana so a janye duk wata kara da ke gaban Alkali kafin a dawo da INTELS. Sannan an ja-kunne a kan yiwuwar saba doka da cin amana.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

Sannan hukumar BPP tayi gargadi a kan kyale INTELS ya ci karensa babu babbaka. Rahoton yace ma’aikata da gwamnatin tarayya sun yi gum a kan maganar.

An samu sabani a 2019

Yarjejeniyar Integrated Logistics Services Limited da gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NPA ya kare ne a 2019, bayan tsawon shekaru 13 suna aiki tare.

Kamfanin Integrated Logistics Services Limited ya samu biliyoyin kudi da wannan kwangila da ya yi, yayin da ita gwamnatin tarayya ta rasa tulin kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel