Atiku: Hukumar NPA ta kwace kwangilar karbar haraji daga hannu kamfanin INTELS

Atiku: Hukumar NPA ta kwace kwangilar karbar haraji daga hannu kamfanin INTELS

Bayan kusan shekaru biyu an tataburza tsakanin gwamnatin Buhari ta hannun hukumar kula tashoshin jiragen ruwa na Najeriya (NPA) da kamfanin nan na Intels da ake rade-radin cewar na Atiku ne, NPA ta kawo karshen dukkan wata yarjejeniya da kamfanin ya kulla da gwamnatin tarayya a kan sa ido da karbar haraji daga kamfanonin dake safarar danyen man fetur da sinadarin iskar gas.

Kamfanin Intels ya sami kwangilar ne a shekarar 2007, a karshen zango na biyu na mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo. Ana zargin cewar tsohon mataimakin shugabann kasa, Atiku Abubakar, ne ya bawa kamfanin Intels kwangilar karbar haraji daga hannun kamfanonin dake safarar danyen man fetur da sinadarin iskar gas, wacce aka kara sabunta ta a shekarar 2011.

A wata wasika mai dauke da kwananan watan 29 ga watan Maris da aka aike wa babban manajan kamfanin Intels, NPA ta ce ta yanke shawarar karbe kwangilar daga hannun kamfanin ne bisa dogaro da sashe na 8 (C) na yarjejeniyar da kamfanin ya kulla da gwamnatin tarayya.

Atiku: Hukumar NPA ta kwace kwangilar karbar haraji daga hannu kamfanin INTELS
Shugabar Hukumar NPA; Hadiza Bala Usman
Source: Depositphotos

A wata takarda mai dauke da kwanan watan 27 ga watan Maris, 2019 da shugabar hukumar NPA, Hadiza Bala Usman, ta aika wa kamfanin Intels ta hannun ofishin babban darektan kudi na NPA, Mohammed Bello-Koko, hukumar ta zargi kamfanin da kin yin biyayya ga umarnin shugaban kasa a kan asusun bai daya (TSA) tare da kin saka harajin $145,849,309.33 da kamfanin ya karba daga watan Nuwamba na shekarar 2017 zuwa watan Oktoba na shekarar 2018 a susun TSA na gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Kasar Indonesia za ta koro matar El-Rufa'i da dan sa gida

A cewar Bello-Koko, sashe na 4.1 na yarjejeniyar dake tsakanin Intels da gwamnatin tarayya ya yi bayanin cewar kamfanin zai saka dukkan harajin da ya karba a aljihun gwamnati ta hanyar zuba su a asusun TSA dake dukkan bankunan kasar nan, wanda kuma daga bisani zasu saka kudaden a asusun gwamnatin tarayya dake babban bankin kasa (CBN).

Ya bayyana cewar Intel ta gaza saka jimillar kudi $55.72m da ta bayyana ta karba a watan Fabarairu na shekarar 2019, kazalika ba ta saka $145.84 da ta aika takardar ta na nema wasu kamfanoni su biya ta ba.

A cewar takaradar, cigaba da kin yin biyayya ga yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da Intels ne ya tilasta hukumar NPA janye batun kwangilar daga hannun kamfanin baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel