Sanusi, Minista za su jagoranci tattaro Biliyan 10 domin a bunkasa kiwon lafiya a Najeriya

Sanusi, Minista za su jagoranci tattaro Biliyan 10 domin a bunkasa kiwon lafiya a Najeriya

  • Nigerian Institute of Medical Research tana neman kudi domin tayi bincike
  • Gidaunyar za tayi nazari a kan cututtukan da ke kashe mutane a yankin Afrika
  • Muhammadu Sanusi II yana cikin wadanda aka ba nauyin tattara gudumuwan

Legas-Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II za su taimaka a inganta lafiya.

Premium Times tace tsohon gwamnan jihar Legas da na babban bankin kasa na CBN za su tattara gudumuwar kudi domin a gudanar da binciken lafiya.

Wadannan Bayin Allah sun sha wannan alwashi a lokacin da gidauniyar Nigerian Institute of Medical Research ta shirya wani taro a Garin Legas.

Khalifa Muhammadu Sanusi da Babatunde Fashola SAN sun amince su tara Naira biliyan 10 daga wajen ‘yan Najeriya da kasar waje domin wannan aiki.

Read also

Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu

Sanusi, Minista za su jagoranci tattaro Biliyan 10 domin a bunkasa kiwon lafiya a Najeriya
Khalifa Muhammadu Sanusi II
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda aka zaba su yi wannan aiki

Yayin da aka zabi Babatunde Fashola a matsayin shugaban majalisar da ke kula da gidauniyar, Sanusi yana cikin masu sa ido tare da wasu likitoci biyu.

Manyan likitocin da za su yi aiki da Khalifan na mabiya Tijjaniya su ne Oye Gureje da Emmanuel Idigbe.

Rahoton yace fitaccen ‘dan jaridar nan, Moji Makanjuola yana cikin majalisar amintattun NIMR.

Makasudin wannan aiki

Gidauniyar NIMR ta na so ayi binciken cikin gida domin magance matsalolin lafiyan da suke damun kasashen Afrika irinsu hawan jini da ciwon sukari.

Darekta Janar na gidauniyar Farfesa Babatunde Salako yace suna fama da karancin kudin bincike, a dalilin haka dole suke yin bincike a kasashen ketare.

Sanusi wanda ya halarci taron ya yabi kokarin shugabannin cibiya, yace ana fama da matsalar mutuwar jarirai, sannan mutane na yawan mutuwa da wuri.

Read also

Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi domin aikin wutan Mambilla a shekarar 2022

Fatima Buhari ta shiga majalisar CIFCFEN

A ranar Talatar nan aka ji cewa Fatima Muhammadu Buhari ta samu shiga cikin majalisar amintattun CIFCFEN. Fatima tana cikin 'ya 'yan shugaban kasa.

An yi bikin rantsar da Fatima Buhari da wasu mutane 17 a Mabushi, babban birnin tarayya Abuja.

Source: Legit.ng

Online view pixel