Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu

Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu

  • Zakakuran sojojin Najeriya sun bankado wani farmaki da 'yan ta'addan ISWAP suka kai Aulari
  • Sojojin sun sakarwa 'yan ta'addan wuta yayin da suka runtuma zuwa cikin dajin Sambisa
  • Tuni jirgin yaki ya bi miyagun inda ya dinga ragargazarsu tare da lalata motocin yaki hudu

Borno - Dakarun sojin Najeriya a safiyar Lahadi sun bankado harin da 'yan ta'adda suka kai garin Aulari, jaridar PRNigeria ta ruwaito.

Majiyoyin sun kara da bayyana cewa, mayakan ta'addanci na kungiyar ISWAP ne suka yi kokarin kwace garin Aulari wanda ya ke da nisan kilomita 11 daga yammacin Bama.

Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu
Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
Sun ce: "Sojojin rundunar Operation HADIN KAI cike da nasara suka bankado farmakin yayin da 'yan ta'addan suka tsere tare da runtumawa zuwa dajin Sambisa."

Kara karanta wannan

Dubun wasu mutane masu kaiwa yan fashin daji kayan abinci ya cika a Abuja

Wani jami'in sirri daga rundunar sojin ya tabbatar da wannan cigaban ga PRNigeria.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce: "Wani jirgin dakarun NAF ya tashi domin bibiyar 'yan ta'addan da suka tsere. Cike da sa'a kuwa ya hango su da motocin yaki guda hudu wadanda aka yi wa ruwan wuta.
"Bayan ruwan wutan da aka yi wa motocin hudu, uku daga ciki sun kone kurmus yayin da sauran ba su iya zuwa ko ina.
“An sheke wasu daga cikin 'yan ta'addan a yayin wannan artabun yayin da wasu suka tsere a firgice."

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

A wani labari na daban, Dakarun sashi na 5 na atisayen Golden Dawn da aka tura Enugu sun sheke mutum 3 da ake zargin 'yan awaren kudu ne da aka fi sani da IPOB, wadanda suka kai wa 'yan sanda farmaki kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar da kakakin dakarun sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar tace, zakakuran sojin sun yi artabu da miyagun kuma suka fi karfinsu, lamarin da yasa suka arce.

"Dakarun sojin ba su kakkauta ba suka bi su tare da cigaba da zuba musu ruwan wuta. Uku daga cikin 'yan bindigan da ke tuka motoci biyu kirar Hilux da Hummer bus ne suka bakunci lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: