2023: Ba laifi bane idan PDP ta zaɓi ɗan takarar shugabancin ƙasa daga Arewa, Sanatan Kudu

2023: Ba laifi bane idan PDP ta zaɓi ɗan takarar shugabancin ƙasa daga Arewa, Sanatan Kudu

  • Dangane da zaben shugabancin kasa na 2023 dake karatowa, tsohon bulaliyar majalisar tarayya ya magantu
  • A cewar Sanata Roland Owie, daidai ne dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP ya kasance dan arewa
  • Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da shi a Benin, babban birnin Edo

Jihar Edo - Batun zaben shugaban kasa na 2023 da ke ta karatowa, tsohon bulaliyar majalisa, Sir Roland Owie, ya bukaci shugabannin jam’iyyar PDP su tsaya tsayin-daka wurin tsayar da dan arewa a matsayin dan takarar ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Owie ya yi wannan kiran ne yayin tattaunawa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, inda ya ce tun 1999 ‘yan kudu su ke ta shugabantar kasar nan, tsawon shekaru 14 kenan yayin da shekaru kasa da 3 kacal ‘yan arewa su ka yi su na shugabanci.

Read also

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

2023: Ba laifi bane idan PDP ta zaɓi ɗan takarar shugabancin ƙasa daga Arewa, Sanatan Kudu
Tutar jam'iyyar PDP. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Kamar yadda Owie ya bayyana bisa ruwayar Daily Trust:

“PDP ce kadai jam’iyyar da ta yarda da hadin kai a kasar nan, don haka ta tsayar da dan arewa a matsayin shugaban kasa. Kada a bar son kai ya dakatar da PDP daga yin abinda ya dace.”
“Tun shekarar 1999, ta Chief Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, kudu ta kwashe shekaru 14 tana mulki yayin da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’Adua ya yi kasa da shekaru 3 yana mulki.”

Yace yanzu ne ya kamata PDP ta tsayar da dan arewa

Owie ya bayyana cewa rashin adalci ne da PDP ta yi wa kudu maso yamma a ranar zaben 12 ga watan Yuni da aka rushe sakamakon zaben da marigayi Chief MKO Abiola ya lashe, shugabancin da aka mika ga Obasanjo.

Read also

2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa

Ya kara da cewa a wannan zaben ne manyan jam’iyyu 2 da ake ji da su suka tsayar da ‘yan kudu maso yamma, inda PDP ta tsayar da Olusegun Obasanjo yayin da APP/AD ta tsayar da Olu Falae. Mun koma zabe ne don samar da hadin kai da zaman lafiya.

Kamar yadda ya ce:

“Obasanjo ya ci zaben duk da be samu a yankin sa da kudu maso yamma ba sannan ya kwashe shekaru 8 ya na mulki. Daga nan shugabanci ya koma arewa saidai Marigayi Yar’Adua ya yi shekaru 2 da watanni kafin ya amsa kiran Ubangijin sa. Mataimakin sa ya dora akai kuma ya tsaya takara ya ci.
“Idan ka kirga, tun daga 1999 zuwa yanzu PDP, kudu ta kwashe shekaru 14 ta na mulki. Don haka adalci ne yanzu PDP ta tsayar da dan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa.”

A cewar sa, idan ba karba-karba ake yi ba, dakyar kudu ta sake samar da shugaban kasa saboda arewa ta fi yawan masu zabe fiye da kudu.

Source: Legit

Online view pixel