Bayan mika shugabancin PDP Arewa, an sanar da miliyoyi a matsayin kudin sayen fom

Bayan mika shugabancin PDP Arewa, an sanar da miliyoyi a matsayin kudin sayen fom

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, ta fara sayar da fom din tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar
  • Jam'iyyar ta bayyana kudaden da za a kashe wajen fom din mukamai da dama na ashugabancinta
  • Tuni dama jam'iyyar ta mika kujerar shugabancinta ga yankin Arewacin Najeriya a makon jiya

Abuja - Jam'iyyar PDP ta sanar da cewa, ta fara sayar da sayar da fom na tsayawa takarar mukaman shugabancin jam'iyyar, inda jam'iyyar ta bayyana farashin daban-daban ga mukamai na NWC, Vanguard ta ruwaito.

Yayin da fom din kujerar shugaban jam'iyya za ta kasance akan Naira miliyan 5, mataimakin shugaban jam'iyya da na sakatare na kasa za a sayar dasu a kan kudi Naira miliyan uku kowanne.

Fom din wasu ofisoshi a cikin NWC da suka hada da sakataren yada labarai na kasa, mai binciken kudi na kasa, sakataren kudi na kasa, shugaban matasa na kasa, ma’aji na kasa da mai ba da shawara kan harkokin doka, za su same shi a kan kudi naira miliyan biyu.

Read also

Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

Jam'iyyar PDP ta sanya kudin tikitin tsayawa takara a zaben 2023
Jam'iyyar PDP ta fara sayar da fom din shugabancinta | Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Za a samu fom na wasu ofisoshin (wakilai) na kasa kan kudi N750, 000 kowanne.

Atiku da Saraki na kitsa kwace PDP daga gwamnoninta, su sake dawo da Secondus

Rahoton da jaridar ThisDay ta fitar ya nuna cewa shugabannin Arewa na tunanin yin amfani da zabin da aka amince da shi na zaben shugaban jam'iyyar PDP, bayan karkatar da ofishin ga yankin.

Rahoton, duk da haka, ya nuna cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark da tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido sune na gaba-gaba a takarar neman mukamin.

Sai dai, masoya ga Atiku Abubakar da Dakta Bukola Saraki sun zafafa yunkurin da ake zarginsu na karkatar da shugabancin jam'iyyar tare da datse bukatar dan takarar shugaban kasa daga kudanci.

Read also

Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya

Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

A tun farko, Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.

Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.

Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.

Source: Legit

Online view pixel