Fasto ya yi wa Gwamnoni 2 mummunan baki saboda sun dawo APC, yace Umahi ya koma PDP

Fasto ya yi wa Gwamnoni 2 mummunan baki saboda sun dawo APC, yace Umahi ya koma PDP

  • Primate Elijah Ayodele ya yi wa David Umahi da Ben Ayade albishiri maras dadi
  • Babban malamin kiristan yace gwamnonin za su yi nadamar barin jam’iyyar PDP
  • Fasto Elijah Ayodele ya ba Umahi shawarar ya koma PDP ko ya ga takaici a 2023

Lagos - Babban limamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya gabatar da wasu hasashe da ya yi a game da zabe mai zuwa.

Daily Post tace Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade da takwaransa na Ebonyi, Dave Umahi, za su ciza yatsa a 2023.

Da yake huduba a ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, 2021, Fasto Ayodele yace burin gwamna David Umahi na shiga fadar shugaban kasa ba zai kai ga ci ba.

Read also

Jam’iyyar PDP tana fuskantar barazana, Uche Secondus yace ba zai janye kara a kotu ba

Elijah Ayodele ya fitar da jawabi ne ta bakin hadiminsa, Oluwatoyin Osho, inda yace Umahi zai gamu da takaici a tafiyar siyasarsa gabanin babban zaben 2023.

A jawabin da ya fitar, Fasto Ayodele ya ba gwamnan na jihar Ebonyi shawarar ya koma jam’iyyar PDP da ya bari, muddin yana so a rika dama wa da shi a siyasa.

Gwamnan Ebonyi
Buhari da Gwamna Dave Umahi Hoto: www.channelstv.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai an manta da sunanka a APC - Ayodele ga Umahi

Malamin addinin yace za a manta da labarin gwamnan idan har ya cigaba da zama a jam’iyyar APC.

“Burin gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, na zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba zai kai ga ci ba, za a jefa shi a matsala.”
“Sannan kuma jam’iyyarsa ba za ta kawo jiharsa (Ebonyi) a zaben 2023 ba.”
“Daf da karshen wa’adinsa, hadimansa shi da abokan siyasa za su ba shi mamaki. Idan yana so a cigaba da yi da shi, ya koma jam’iyyar da ya baro ko a manta da shi.” - – Ayodele.

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Faston yace shi ma gwamna Ben Ayade zai sha kunya, musamman a zaben 2023. A cewar malamin addinin, masoyansa za su juya masa baya, kuma zai yi nadama.

Takarar kujerar shugaban jam'iyyar PDP

A makon nan aka ji cewa za a gwabza tsakanin David Mark, Ahmad Makarfi, Ibrahim Shema, Ibrahim Idris wajen a zaben shugaban jam'iyyar adawa ta PDP na kasa.

Ana rade-radin cewa Sanata Dino Melaye ya shiga cikin masu sha’awar rike jam'iyyar hamayyar. Melaye ya wakicli Kogi ta yamma a majalisar dattawa kafin ya bar APC.

Source: Legit

Online view pixel