Dadadden Hadimin Buhari ya yi babban rashi, Mahaifiyar Sarki Abba ta bar Duniya

Dadadden Hadimin Buhari ya yi babban rashi, Mahaifiyar Sarki Abba ta bar Duniya

  • Mahaifiyar Sarki Abba ta rasu, an yi mata sallah a garin Jimeta a ranar Lahadi
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana kan mutuwar Aishatu Abba
  • Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa, sannan ya tura wakilai zuwa wajen jana’iza

Abuja - Fadar shugabar kasa tace shugaban kasa, Mai girma Muhammadu Buhari ya yi magana game da mutuwar mahaifiyar hadiminsa, Sarki Abba.

Muhammadu Buhari ya girgiza da jin labarin rasuwar mahaifiyar Sarki Abba. Malam Garba Shehu ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Facebook.

Da yake jawabin a ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, 2021, Malam Shehu yace Hajiya Aishatu Abba ta rasu bayan doguwar jinya, ta rasu tana da shekara 96.

Wannan Baiwar Allah ta rasu a Yola, ta bar ‘ya ‘ya biyu da jikoki da dama. A cikin ‘ya ‘yan ta akwai mai taimaka wa shugaban kasa wajen harkokin gida.

Read also

Ya zama dole a ba yankin Kudu takarar shugaban kasa a zaben 2023 inji Jigon PDP

Hadiman shugaban kasa ne suka wakilci Muhammadu Buhari a jana’izarta da aka yi a Adamawa.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

Wakilan da Buhari ya tura wajen sallar jana'iza

Wadanda suka wakilci Buhari a wajen jana’iza sun hada da Ya'u Darazo, Garba Shehu, Lawal Kazaure, da likitan fadar shugaban kasa Dr. Suhayb Rafindadi.

Sauran ‘yan tawagar sune: Idris Ahmed, Tijjani Umar, Air Commodore Y. A. Abdullahi da Abdulmumin Bello.

“Mun yi rashin jagorar al’umma, mai kirki da kyauta. Jama’a sun yi koyi da halin ta na kyauta a rayuwa. Tayi tasiri a rayuwar mutane da-dama.”
“Ta’aziyya ta ga Sarki Abba da iyalinsa, wanda suka yi rashin babban bango. Allah (SWT) Ya yi mata rahama, kuma Ya karbi ayyukan ta na alheri.”

Shehu yake cewa shugaan kasar ya aika ta’aziyyarsa ga masarauta da gwamnati da daukacin al’ummar jihar Adamawa a kan wannan rashi da suka yi.

Read also

‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

Tsohon gwamnan Adamawa, Sanata Jibrilla Bindow, Galadima da Dan Iyan Adamawa suna cikin dubban mutanen da suka yi wa marigayiyar sallah a Jimeta.

Cikakken jawabin Malam Garba Shehu

Frank ya caccaki gwamnatin Buhari

A ranar Litinin aka ji cewa tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Timi Frank, ya yi Allah wadai da kasafin kudin shekarar 2022.

Kwamred Timi Frank yace babu ribar da talaka zai samu daga kasafin kudin shekarar 2022 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban 'yan majalisa.

Source: Legit.ng

Online view pixel