Yanzu-yanzu: Yan Najeriya na korafin layukan MTN sun daina aiki a Abuja, da wasu jihohin Najeriya
Yan Najeriya sun yi korafi kan yadda layukan wayoyinsu na MTN suka daina aiki da yammacin ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba, 2021.
Mutane da dama daga birnin taraya sun bayyana cewa sun gaza kiran 'yan uwa da abokan arziki a waya.
Legit ta samu ji daga bakin wani ma'aikacin MTN wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya tabbatar da cewa akwai matsalar Network a fadin tarayya amma ana gyarawa.
A jawabin da kamfanin ya saki, ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala amma ana kan gyara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad yace:
"Ba MTN dinka kadai ne baya aiki ba, kuma ba unguwarku kadai bace. yawancin masu amfani da MTN na fuskantar matsalar kira da ranan nan."
Wani mazaunin unguwar Lokogoma a Abuja, Usman, ya bayyana mana cewa:
"Na kasa kira ga layin MTN tun dazu."
Hakazalika wata dattijuwa mazauniyar Efab Estate dake Abuja tace:
"Shin layukan MTN na yi kuwa?"
Aisha Muhammad ta bayyana mana cewa:
"Ina ta kokarin kira mahaifiyata tun dazu amma abun ya gagara"
Abubakar Adamu yace:
Harda Manan jahar Niger
Kabir Hamisu Daura yace:
Har anan jihata ta katsina yanzu haka layi na baya tafiya yasa mini emergency
Auwalu Muhd Bashir Kurugu
"Harda Okene kogi state"
Asali: Legit.ng