Magoya baya sun damu da abubuwan da ke faruwa a APC, sun rubuta wa Buhari wasika
- The Concerned APC Stakeholders ta koka a kan halin da jam’iyyar APC ta ke ciki
- Kungiyar magoya-bayan tace jam’iyyar ta bi layin da ya kashe PDP a zaben 2015
- Abubakar Sidiq Usman ya rubuta takardar kai kuka zuwa ga shugaban Najeriya
Abuja - Wata kungiyar siyasa mai suna The Concerned APC Stakeholders ta nuna takaicinta game da yadda abubuwa suke tafiya a jam’iyyar APC mai mulki.
Jaridar nan ta Daily Trust ta rahoto kungiyar Concerned APC Stakeholders tana cewa APC ta kama layin da jam’iyyar PDP ta bi gabanin zaben shekarar 2015.
Wadannan magoya baya sun aika takarda ta musamman zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, suna kukan cewa jam’iyyarsu ta APC ta saki layinta.
Abubakar Sidiq Usman wanda ya sa hannu a wannan wasika, ya shaida wa shugaban kasar cewa wasu na-banza suna amfani da sunansa, suna bata jam’iyya.
2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja
An rahoto Abubakar Sidiq Usman yana bada misali da zabukan mazabu da na kananan hukumomin da aka gudanar, yace ba ayi adalci a zabukan ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me wasikar 'yan The Concerned APC Stakeholders ta kunsa?
“Ya mai girma shugaban kasa, muna so mu tuna maka da yadda PDP ta rasa mulki a dalilin amfani da karfi da wasu manyan jam’iyyar suka rika yi.”
“Wasu sun rika tsoma hannuwansu a kan duk abin da ya shafi lamarin jam’iyya, suka hana sauran mutanen da ke da rinjaye damar a dama da su.”
“Wadannan abubuwan da aka ambata na karfa-karfa sun jawo jam’iyyar ta mutu, ta sha kashi a 2015. Muna tsoron APC ta hau layin da ya rusa PDP.”
Ayi gyara, ko a gamu da matsala
Abubakar Usman ya yi kira ga shugaban kasar ya ceci jam’iyyar APC, ya share wa dubban magoya bayanta hawaye domin yana da karfin ikon yaye matsalar.
A madadin Concerned APC Stakeholders, Usman yace ana tsoron APC za ta iya watse wa bayan Buhari ya bar ofis a 2023, muddin shugaban kasar bai yi komai ba.
Ana yi wa Tinubu kamfe
Idan aka koma Legas, kun ji cewa kungiyar magoya baya ta SWAGA 23 ta kaddamar da yakin neman zaben Bola Tinubu, kuma Jide Sanwo-Olu ya ba tafiyar karfi.
Gwamna Sanwo-Olu ya tofa albarka ga masu yi wa Bola Tinubu yakin zama Shugaban Najeriya, yace tsohon gwamnan na Legas cikakken 'dan kishin kasa ne.
Asali: Legit.ng