2023: Gwamnan APC ya ba takarar Asiwaju Bola Tinubu gagarumar goyon-baya gadan-gadan

2023: Gwamnan APC ya ba takarar Asiwaju Bola Tinubu gagarumar goyon-baya gadan-gadan

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya halarci taron yakin neman zaben Bola Tinubu
  • Kungiyar SWAGA ta fara yi wa Bola Tinubu yakin zama Shugaban kasa a 2023
  • Jide Sanwo-Olu ya yabi tsohon Gwamnan na Legas, ya kira sa ‘Dan kishin-kasa

Lagos - Mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ‘dan kishin kasa, wanda yake son kawo cigaba.

Jaridar The Cable tace Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wannan a lokacin da kungiyar SWAGA 23 ta kaddamar da shirin yakin neman zaben Tinubu.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, 2021, kungiyar Southwest Agenda 2023 ta shirya biki domin kaddamar da yi wa Tinubu kamfen domin zama shugaban kasa.

Sanwo-Olu yana cikin wadanda suka halarci wannan biki, inda aka ji ya na yaba wa tsohon gwamnan na jihar Legas, kuma babban mai gidansa a siyasa.

Read also

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Inda Tinubu ya sha bam-bam da sa’o’insa

Gwamnan ya bayyana cewa Bola Tinubu yana da wasu halaye da suka sa ya yi fice a siyasar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace Jide Sanwo-Olu ya yaba da irin gyaran da gwamnatin Tinubu ta kawo wa Legas a lokacin da ya yi mulki na shekaru takwas tsakanin 1999 da 2007.

'Yan SWAGA 2023
Taron kaddamar da tafiyar SWAGA 2023 Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

Sanwo-Olu yace har yanzu da wannan bazar ta babban jigon na jam’iyyar APC mai mulki su ke rawa.

“Asiwaju Tinubu mutum ne mai hangen nesa, son aiki da kokarin aiwatarwa. Wadannan abububuwa uku suka sa yayi zarra a cikin sa’anninsa a siyasa yau.”
“Ba abin mamaki ba ne don hasken Tinubu ya zarce Legas, shekaru takwas da ya yi a matsayin gwamna (na jihar Legas), ya kafa turakun da muke bi ta kai a yanzu.”

Read also

Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari

“’Dan kishin kasa ne a wajen tunaninsa, kuma mai son kawo gyara a wajen aikinsa.”

Sanwo-Olu ya yabi SWAGA, yace kungiyar za ta taimaka wa Tinubu ya zama shugaban kasa. PM News tace Mataimakinsa, Hamzah Lawal ya yi jawabi a wajen taron.

Joe Igbokwe ya ja-kunnen Ibo

A makon nan ne aka yi hira da jigon APC na jihar Legas, Joe Igbokwe inda ya fada wa ‘Yan Kabilar Ibo cewa babu wanda zai yadda za su karbi Shugabanci a 2023.

‘Dan siyasar ya gargadi mutanensa cewa dole su hada-kai da sauran kabilun Najeriya. Sai dai Igbokwe ya yarda ba a iya wa mutanen yankin kudu maso gabas adalci.

Source: Legit

Online view pixel