Kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa tace akwai shirin kawo matsala a zaben 2023
- Kungiyar CUPP tace akwai makarkashiya a game da zabe mai zuwa na 2023
- Ikenga Imo Ugochinyere yace akwai yiwuwar a ki amfani da na’urar zamani
- Kakakin kungiyar ya bayyana cewa ana ba ‘Yan majalisar tarayya cin hanci
Abuja - Kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasar Najeriya, CUPP, ta sanar da jama’a cewa ta samu labarin kawo wa zabe mai zuwa na shekarar 2023 cikas.
A wajen wani taron manema labarai da aka shirya a garin Abuja, kakakin CUPP, Mista Ikenga Imo Ugochinyere yace akwai shirin a hana ayi adalci a zaben.
Leadership ta rahoto Ikenga Imo Ugochinyere yana cewa ba za a karasa sa hannu a dokar zabe ta yadda hukumar INEC za tayi amfani da na’urorin zamani.
Imo Ugochinyere yake cewa ana so da karfi da yaji a ki yin aiki da na’urori wajen tattara kuri’u.
Jaridar ta rahoto mai magana da bakin kungiyar yana cewa ana ba ‘yan majalisa cin hanci domin a ga an yi watsi da batun yi wa dokar zabe kwaskwarima.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mun samu kishin-kishin - Ikenga Imo Ugochinyere
“Bayanan da suke zuwa mana shi ne, ana hada wa da ba ‘kwamitocin ‘yan majalisa cin hanci cikin dare domin su ga ba a bari an yi amfani da na’ura a zabe ba.”
Ugochinyere yace ‘yan majalisa sun yarda su yi ta jan maganar yi wa dokar zabe garambawul har zuwa lokacin da za su tafi dogon hutu a shekara mai zuwa.
“Wannan cin mutunci ne ga ‘yan Najeriya, ganin cewa an fara aikin gyara dokar zabe tun shekarar 2016, kuma har bayan shekaru biyar ba a kammala ba.”
Kungiyar ta CUPP tace idan maganar ta kai lokacin, ba za a iya yi wa dokokin zabe wata kwaskwarima ba kamar yadda dokokin ECOWAS suka tanada.
A madadin CUPP, Ugochinyere yace mutanen Najeriya ba za su yarda a hana hukumar INEC amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da zaben na 2023 ba.
Uzor Kalu ya yi magana kan 2023
A makon nan aka ji Sanatan jihar Abia ta Arewa Orji Uzor Kalu ya na bayani cewa bai da sha’awar zama Shugaban Najeriya a 2023, amma jama’a su na tunzura shi.
Uzor Kalu yace yana so ne ya zarce a kujerar da yake ta ‘Dan Majalisar Dattawa ba ya rike kasa ba.
Asali: Legit.ng