Saboda a murdewa APC zaben Gwamna ake shirin kafa dokar ta baci a Anambra inji PDP
- Jam’iyyar PDP ta maida martani a kan batun sa dokar ta-baci a jihar Anambra
- Kakakin PDP ya zargi gwamnatin tarayya da shirin yin magudi a zaben gwamna
- Kola Ologbondiyan ya fitar da jawabi, ya yi kira a kawo karshen matsalar tsaron
Abuja – Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP tayi gargadi a kan kafa dokar ta-baci a jihar Anambra yayin da ake shirin gudanar da zaben sabon gwamna.
A wani jawabi da ya fitar, mai magana da yawun bakin PDP ta kasa, Kola Ologbondiyan, yace gwamnatin tarayya ta daina tunanin sa dokar ta-bacin.
Gidan talabijin na Channels TV ya rahoto sakataren yada labarai na jam’iyyar adawar yana zargin gwamnatin APC da kawo wannan domin a murde zabe.
Ologbondiyan ya yi wa jawabin take da Gwamnatin tarayya ta birne tunanin kakaba dokar ta baci a Anambra, yayin da ake shirin zaben 6 ga watan Nuwamba.
Jaridar Premium Times ta rahoto Ologbondiyan yana zargin APC da yunkurin tafka magudi a zaben sabon gwamnan ta yadda za ta kafa gwamnati a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin da Kola Ologbondiyan ya fitar
“Jam’iyyar PDP tayi imani cewa neman kafa dokar ta-baci a jihar Anambra, dabara ce ta gwamnatin APC ta yadda za ayi wa mutane murdiya, a murde zabe zaben gwamna domin APC da ‘dan takararta su samu nasara.”
“Jam’iyyarmu tana bukatar APC da gwamnatinta ta yi bayanin abin da ya jawo karu war rashin tsaro a jihar Anambra a lokacin da ake shirin yin zabe.”
Sakataren yada labaran na jam’iyyar PDP yace an dasa irin rikice-rikicen da ake gani a Anambra ne saboda jam’iyyar APC ta samu damar dare wa kan mulki.
PDP tace za a iya shawo kan matsalar tsaro ba tare da sa dokar ta-baci ba, tayi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta APC tayi abin da ya kamata.
A karshen jawabin, jam’iyyar adawar tayi kira ga mutanen jihar Anambra su kwantar da hankalinsu.
Magoya baya suna taya Tinubu kamfe
A farkon makon nan aka ji fastocin babban jigon jam'iyyar APC a kudu maso yammacin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu sun fara cika wasu lungunan jihar Legas.
An ga fastocin Bola Tinubu a Ojota, Maryland, Ketu Ikeja, da Lagos Island. Abin tambayar shi ne wa zai zama abokin takarar babban ‘dan siyasar a APC a 2023.
Asali: Legit.ng