Sarkin Argungu zai gwangwaje Lai Mohammed da sarautar Kakakin Kebbi
- Alhaji Mohammed Mera, Sarkin Kebbi, zai gwangwaje ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed, da sarauta
- Mai Martaba Mohammed Mera zai nada Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi, babbar sarautar mai ma'anar jakadan Kebbi
- Za a yi wa ministan wannan sarautar ne a ranar 25 ga Satumba sakamakon gudumawar da yake baiwa habaka al'adu
FCT, Abuja - Sarkin Argungu na jihar Kebbi, Mohammed Mera, a ranar 25 ga watan Satumba za a nada shi ministan al'adu da labarai, Lai Mohammed da babbar sarautar Kakakin Kebbi.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da Tsangayar karamci da yawon bude ido, NIHOTOUR, a ranar Juma'a a Abuja ta fitar, wacce ta samu sa hannun Ahmed Sule, daraktan yada labarai da hulda da jama'a.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar 7 ga watan Maris, 2020, yace Sarkin ya baiwa Lai Mohammed Kakakin Kebbi, ma'ana jakadan al'adu na Kebbi.
Sarkin ya sanar da bada sarautar ga Ministan a Abuja yayin kaddamar da jerin shirye-shiryen na gasar kamun kifi na Argungun na 2020 wanda aka yi daga 11 ga watan Maris zuwa 14.
Yaushe za a yi nadin sarautar?
Sule yace shirye-shiryen sun yi nisa domin nada ministan babbar sarautar, Daily Nigerian ta ruwaito.
Hukuncin nada Mohammed sarautar daga masarautar Argungun kamar yadda yace, an kai ga matsaya ne bayan taron da aka yi na masarautar tare da duba kokarin ministan wurin tabbatar da bayyanar al'adun Najeriya ga duniya.
Kamar yadda takardar tace, nadin ministan a matsayin Kakakin Kebbi yana daga cikin jerin shagalin wannan shekarar na ‘World Tourism Day’ wanda gwamnatin jihar Kebbi za ta dauka nauyi a ranar 27 ga watan Satumba.
Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta
Majalisar jihar Kaduna ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta, Mukhtar Isa-Hazo, dan majalisa mai wakiltar mazabar Basawa.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an dakatar da Hazo tare da wasu 'yan majalisa uku fiye da shekara daya da ta gabata.
Hukuncin ya biyo bayan wata bukata da Ahmad Muhammad, dan majalisa mai wakiltar mazabar Zaria da Kewaye ya mika yayin zaman majalisar a ranar Laraba a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng