Ba za'a sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijistan layin waya ba, Hukumar NCC

Ba za'a sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijistan layin waya ba, Hukumar NCC

  • Sabuwar dokar hukumar sadarwan Najeriya ta haramta yan kasa da shekaru 18 mallakar layukan waya
  • Hukumar NCC ta ce dokokin kafata sun bata karfin yin haka
  • Daga yanzu za'a daina sayarwa yan kasa da shekaru 18 layin waya

Abuja, FCT - Daga yanzu zaa daina yiwa yan Najeriya masu shekaru kasa da 18 rijisan layukan waya kuma ba zasu iya mallakar SIM ba a Najeriya, hukumar sadarwan Najeriya NCC ta bayyana.

Punch ta ruwaito cewa wannan umurni na kunshe cikin sabuwar dokar rijistan layukan waya da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

A wallafar, hukumar ta umurci kamfanonin sadarwa daga yanzu kada su sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijista.

A cewar sanarwar:

"Wanda za'a iya wa rijista shine mutumin da bai da kasa da shekaru 18 kuma shine wanda zai iya mallakan layin waya kuma ya iya siyayya daga kamfanin sadarwa mai lasisi."

Kara karanta wannan

Rushe-rushe: Makaranta ta bayyana abin da ya sa aka rugurguza gidajen mutane 160 a Zaria

Hukumar tace ta ta dau wannan mataki ne bisa sashe 70 na dokar kafata na NCC Act 2003.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba za'a sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijistan layin waya ba, Hukumar NCC
Ba za'a sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijistan layin waya ba, Hukumar NCC
Asali: UGC

FG ta ce an hada layukan waya miliyan 180 da NIN

A bangare guda, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) Farfesa Umar Danbatta, ya bayyana adadin layukan wayar tarho da aka hada da Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) a yanzu.

A cewarsa, sama da layukan waya miliyan 180 aka hada a yanzu. Ya bayyana hakan a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa ya fadi wannan ne biyo bayan yiwa 'yan Najeriya sama da miliyan 60 rijista da Hukumar samar da lambar dan Kasa (NIMC) ta yi a cikin bayanan NIN.

Ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabinsa yayin zantawa da Jama'a kan Ka'idoji guda uku kan Tsarin Kare Dokoki a hedikwatar Hukumar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng