Sunday Igboho ya na buƙatar kulawar likitoci cikin gaggawa, Kakakin Igboho ya roƙi Shugaban Jamhuriyar Benin

Sunday Igboho ya na buƙatar kulawar likitoci cikin gaggawa, Kakakin Igboho ya roƙi Shugaban Jamhuriyar Benin

  • Kakakin Igboho, Olayomi Koiki ya ce Sunday Igboho ya na fama da matsanancin ciwo
  • Sakamakon hakan ne ya ce akwai bukatar ya samu kalawar likitoci cikin gaggawa
  • Ya bayyana hakan ne ta takarda wacce ya saki a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba

Jamhuriyar Benin - Mai rajin kafa kasar yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya na bukatar kulawar asibiti cikin gaggawa kamar yadda kakakin sa ya ce.

SaharaReporters ta ruwaito yadda kakakin Igboho, Olayomi Koiki a ranar Talata ya ce Igboho yana fama da ciwo mai tsanani.

Sunday Igboho ya na bukatar kulawar likitoci cikin gaggawa, Kakakinsa
Sunday Igboho. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Kamar yadda Koiki ya saki wata takarda mai taken, “A bakacin Cheif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho’ inda ya yi kira ga gwamnatin jamhuriyar Benin da ta bai wa Igboho damar ganin likita don kulawa da lafiyarsa.

Koiki ya ce shugaban kasar Benin ba zai so wani abu ya faru da Igboho a kasarsa ba

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, takardar ta bayyana kamar haka:

“Bayan tattaunawa da lauyan sa, ina so in tabbatar da yadda yake bukatar kulawa don ba ya da lafiya kuma mu na so mu yi amfani da wannan damar wurin rokon gwamnatin jamhuriyar Benin, Shugaban kasa Patrice Talon, da ya taimaka ya bar Cheif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya samu kulawar likita.
“A halin yanzu ya na fama da matsanancin ciwo, a taimaka wa lafiyar sa. Mun san kai mutum ne da ke son cigaba ga kasar sa. Mun ga abubuwa da dama da ka yi na gyara a kasar ka.

Kara karanta wannan

Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon

“Shugaba Patrice Talon, ka taimaka ka sa hannu a yi gaggawar sakin sa sakamakon ciwon da ke damun sa, ba za mu so wani abu ya same shi ba yana rike a kasar ka.
“Tun ranar 20 ga watan Yulin 2021 Igboho yake rike a kasar ka kuma yana fama da matsanancin rashin lafiya."

Mungode da taimakon ka.

“Za mu so muyi amfani da wannan damar wurin godiya ga lauyoyin sa da kuma duk wanda ya tsaya tsayin daka akan shi a wannan lokaci mai tsanani.”

Yadda lamarin ya auku

Jami’an tsaron jamhuriyar Benin sun kama Igboho da matar sa a Cotonou, jamhuriyar Benin a ranar 19 ga watan Yuli bayan ya tsere daga Najeriya don guduwa daga ‘yan sandan sirrin Najeriya da suke neman sa.

Jami’an tsaro na fararen kaya (DSS) sun nemi Igbo ido rufe bayan sun je har gidan sa da ke wuraren Soka a Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Tun a lokacin kakakin DSS, Peter Afunnaya ya shawarci Igboho ya bayyana kansa.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, Afunnaya ya ce:

“Duk masu ba shi miyagun shawarwari su yi abinda ya dace.
“Ya yi gaggawar kawo kan sa zuwa ga hukuma don babu wanda ya fi karfin doka.”

Saidai ‘yan sanda sun dade da sakin matar Igboho yayin da shi kuma yake rike a hannunsu.

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar damkar masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kudin fansar yaro dan shekara 7, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin inda ya ce sun kama wani Muhammed Abubakar mai shekaru 42 da Clinton Niche mai shekaru 18.

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Oyeyemi ya ce mahaifin yaron, Stephen Ajibili, ya kai korafin satar dan sa, Daniel, da aka yi inda ya ce mahaifiyar sa tana tsaka da aiki da misalin karfe 11:20am aka sace shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel