Wani mutum ya mutu mintuna kaɗan bayan haɗuwa da mahaifinsa a karon farko cikin shekaru 35

Wani mutum ya mutu mintuna kaɗan bayan haɗuwa da mahaifinsa a karon farko cikin shekaru 35

  • An tabbatar da mutuwar wani mutum bayan ya hadu da mahaifin sa a karo na farko cikin shekaru 35
  • Paul Cowell mai shekaru 53 ya tafka hatsari bayan babur din sa ya gwabza karo da babbar mota
  • Diyar sa ta shaida cewa bai wuce minti 10 ba da haduwa da mahaifin sa da ya kwashe shekaru 35 ba su hadu ba

Amurka - An tabbatar da mutuwar wani mutum bayan mintoci kadan da haduwa da mahaifin sa da ya share shekaru 35 ba su hadu ba.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Paul Cowell mai shekaru 56 ya rasa ran sa bayan babur din sa ya gwabza mummunan karo da babbar mota a Isle of Man a ranar 27 ga watan Satumba.

Bayan haɗuwa da mahaifinsa a karon farko cikin shekaru 35, ya rasa ransa
Paul Cowell. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Lance Live ta ruwaito yadda ake zargin rana ce ta hana shi ganin hanya yayin da yake bin wani titi a Mountain Road Guthries.

Diyar matar sa ta ce abin akwai firgitarwa

Diyar matar sa mai shekaru 22, Demi Ramshaw ta bayyana yadda hatsarin ya auku bayan bai wuci mintoci 10 ba da haduwar Paul da mahaifin sa wanda su ka kwashe shekaru 35 ba su hadu ba.

Kamar yadda Ramshaw ta bayyana bisa ruwayar LIB:

“Karo na farko kenan da yaran sa 2 su ka ga kakan su, sai ya nufi kabarin mahaifiyar sa dake kusa da Mountain Road.
“Ni da masoyi na mun samu yaro wanda kwanan sa 12 kenan, don haka karon farko kenan da ya gan shi. Abin akwai ban tsoro. Ina ganin har yanzu abokiyar zaman sa, Nicola a firgice take don har Isle of Man taje musamman don ta gan shi.”

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Yanzu haka an bude wata kafa wacce za a tattara kudi don a samu a birne shi.

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164