Asirin fitattun ‘Yan siyasa da 'Yan kasuwan Najeriya 10 ya tonu a badakalar Pandora Papers

Asirin fitattun ‘Yan siyasa da 'Yan kasuwan Najeriya 10 ya tonu a badakalar Pandora Papers

  • Pandora Papers ya tona asirin wasu shahararrun mutane a kasashen Duniya
  • An samu mutane akalla 10 da ake zargi da boye sirrin dukiyarsu a Najeriya
  • Binciken da aka gudanar ya fallasa ‘Yan siyasa har da wani malamin addini

‘Yan siyasa 336 aka tona asirin barnar da suke tafkawa kamar yadda binciken International Consortium of Investigative Journalists ya nuna.

Kungiyar ICIJ ta ‘yan jarida da suka kware wajen bincike sun wallafa badakalar Pandora Papers da ya tona wa wasu ‘yan siyasa a Najeriya asiri.

Punch tace takardun da aka fitar sun bayyana cewa akwai fitattun manyan da ake ganin darajarsu a cikin wadanda suke aikata ba daidai ba.

‘Yan jarida 600 suka hadu suka yi wannan bincike da ya fallasa asirin mutane a kasashen Afrika takwas, daga ciki har da ‘yan Najeriya har goma.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Kawo yanzu Jaridar Guardia tace a jerin akwai tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a 2019.

Rahoton yace Peter Obi wanda jigo ne a jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ya boye wa hukumar CCB gaskiyar kadarorin da ya mallaka a Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Peter Obi
Peter Obi yana kamfe Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Abin da binciken ya nuna

A jerin akwai wani tsohon Alkalin Alkalan Najeriya da ba a kama sunansa ba. A halin yanzu akwai tsofaffin Alkalin Alkalan kasar bakwai da ke raye.

Har ila yau an samu sunayen wasu tsofaffin gwamnoni har da gwamnoni masu ci. Kuma akwai tsofaffi da ‘yan majalisar tarayya da suke rike da kujera.

Bayan haka an samu sunayen manyan ‘yan kasuwan da suka yi fice da kuma wani shahararren fasto. Haka zalika su ma ba a ambaci sunansu ba tukun.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Kason sauran kasashen Afrika

Kasar Côte d’Ivoire ta samu mutum biyar, Ghana na da uku, sannan Chad, Kenya da Congo sun samu ‘yan siyasarsu biyu da suka shiga wannan badakala.

A Gabon an samu ‘ya siyasa uku, a Angola kuwa akwai ‘yan siyasa tara. Binciken ya tona asirin manyan gwamnati biyu daga Zimbabwe da Afrika ta Kudu.

Kasar Mozambique ce karshe a wannan jeri, akwai ‘dan siyasa daya daga kasar da rahoton ya fallasa.

Sanusi II ya soki tallafin fetur

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi tir da biyan tallafijn fetur da ake yi, yace kuskuren da ake tayi shi ne a dauka Najeriya tana da arziki.

A cewar Sanusi II, saboda wasu manya suna amfana da tallafin mai, shiyasa aka gagara dakatar da tsarin da ya ke ci wa Najeriya biliyoyin kudi duk shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel