Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya ambata a jawabin da ya yi wa 'Yan kasa a ranar samun 'yanci

Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya ambata a jawabin da ya yi wa 'Yan kasa a ranar samun 'yanci

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al’umma jawabin samun ‘yanci
  • Muhammadu Buhari ya tabo abubuwan da suka shafi tsaro da annobar Coronavirus
  • Buhari yayi maganar nasarorin da kasar ta samu da irin kalubalen da ake fuskanta

Abuja - A ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa mutanen kasa jawabi domin bikin murnar ‘yancin-kai.

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin muhimman abubuwan da shugaban kasar ya ambata. Femi Adesina ya fitar da jawabin a shafinsa na Facebook.

1. Kalubale a 2020-21

A jawabin na sa, Mai girma Muhammadu Buhari yace tun bayan yakin basasa, Najeriya ba ta fuskanci kalubalen da ya zarce na shekara daya da rabi da suka wuce ba.

Kara karanta wannan

Asirin fitattun ‘Yan siyasa da 'Yan kasuwan Najeriya 10 ya tonu a badakalar Pandora Papers

2. Tattalin arziki

Shugaban Najeriyar ya bayyana nasarorin da ake samu a tattalin arziki bayan annobar COVID-19. Buhari yace karfin GDP ya zabura da 0.11%, 0.51% da 5.01% a 2021.

3. Harkar gona

Harkar gona yana da muhimmanci wajen yunkurin bunkasa tattalin arzikinmu, ya bada gudumuwar 22.35% da 23.78% a jimillar tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban kasar yace duk da noman da ake yi, farashin abinci na tashi. A dalilin haka ya bada sanarwar matakan da za a dauka domin kayan abinci suyi sauki.

4. Rashin tsaro

A Arewa maso gabas kurum, sama da ‘yan ta’addan Boko Haram 8, 000 sun ajiye makamai. Amma shugaban kasar ya koka game da yadda ake fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Buhari
MUHAMMADU BUHARI Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

5. PIA

A jawabinsa, shugaban kasar ya yi maganar sa hannu a dokar PIA, ya kuma yaba kan alakarsa da majalisar tarayya. Sannan yace za a bude kananan matatun mai a wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

6. Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo

"Cafke Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo ya fallasa wadanda ke goyon bayansu. Mun dage a bankado masu taimaka wa wadannan mutane, daga ciki har da wani ‘dan majalisa.”

7. Twitter

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da Twitter a Najeriya, ya kuma bada umarnin janye dakatarwar bayan kamfanin ya amince da ka’idojin da gwamnati ta gindaya.

8. N- Power

Ganin tasirin tsare-tsaren da gwamnatinsa ta kawo, shugaba Buhari yace an kara adadin wadanda suke amfana da shirin N-Power daga 500,000 zuwa 1,000,000.

Baya ga haka ana ciyar da yara miliyan 10 a makarantu, sannan mata 103, 000 sun samu aikin dafu wa daga tsarin, baya ga dubunnan da suka ci moriyar manufofin.

9. COVID-19

Muhammadu Buhari ya dauki lokaci sosai yana magana a kan annobar COVID-19 da kokarin da gwamnatin Najeriya take yi wajen samar da magunguna ga jama’a.

10. Kokarin gwamnatin APC

A cewar Buhari, daga 1999 zuwa yanzu babu wani gwamnati da tayi kokarin magance matsalolin Najeriya irin ta sa, amma wasu suna manta wa da barnar da aka yi a da.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

Twitter zai cigaba da aiki

A jawabinsa na yau ne aka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a dage daktarwar da aka yi wa Twitter a Najeriya bayan kusan watanni hudu.

Shugaban kasar yace kwamitin da ya kafa ya tattauna da Twitter sun cimma matsaya. A dalilin haka aka dage dakatarwar muddin kamfanin zai bi sharudan da aka sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng