Oct 1: Shugaba Buhari zai yi wa mutanen Najeriya jawabi na musamman ranar bikin samun ‘yanci

Oct 1: Shugaba Buhari zai yi wa mutanen Najeriya jawabi na musamman ranar bikin samun ‘yanci

  • Al’ummar kasar nan za su ji daga bakin Shugaba Muhammadu Buhari a gobe
  • Shugaban kasar zai yi jawabi a ranar da Najeriya ke cika shekara 61 da ‘yanci
  • Femi Adesina ya tabbatar da cewa Buhari zai yi jawabi tun karfe 7:00 na safe

FCT, AbujaShugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi wa al’umma jawabi na musaman a safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, 2021.

Mai girma Muhammadu Buhari zai yi magana da karfe 7:00 na safe a matsayin ayyukan bikin ranar samun ‘yancin kai da Najeriya za tayi a shekarar nan.

Femi Adesina wanda yake magana da yawun bakin shugaban kasa, ya bayyana wannan dazu.

October 1 independence anniversary

Jaridar Punch tace Femi Adesina ya yi wa jawabin da ya fitar take da ‘October 1 independence anniversary: President Buhari to broadcast to the nation.’

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Babban mai taimaka wa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da ‘yan jarida, Adesina yace za a saurari jawabin Buhari a gidajen rediyo da na talabijin.

TVC ta ce manyan gidajen talabijin da kuma rediyo za su dauko jawabin da shugaban kasar zai yi a gidan talabijin na NTA da gidan rediyon FRCN na kasa.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Da jawabin shugaban kasar ne ake sa rai gwamnatin Najeriya za ta fara bukukuwan murnar cika shekara 61 da samun ‘yancin-kai a hannun kasar Birtaniyya.

A al’ada duk shugaban kasar Najeriya ya kan yi bayani a wannan rana mai muhimmin tarihi.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta bada hutu na kwana daya saboda wannan biki. A ranar 1 ga watan Oktoban 1960 ne Najeriya ta zama kasa mai ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

Kafin yanzu an ji cewa gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a wasu wurare a Abuja yayin da ake shirin yin bukuku wa domin murnar cika shekara 61 da ‘yanci.

Tun da Mai girma Muhammadu Buhari ya dawo daga taron majalisar dinki Duniya a Amurka, ba a gan shi a fili ba, ana tunani ya killace kan shi saboda COVID-19.

Ta leko ta koma a NPRA

A jiya aka ji Shugaba Muhammadu Buhari ya maye gurbin Sarki Auwalu da Farouk Ahmed a hukumar man fetur na kasa na NPRA, kafin Auwalu ya shiga ofis

Sarki iAuwalu bai da rabon rike NPRA domin ‘Yan Majalisa za su tantance Ahmad a madadinsa. A satumban nan Buhari ya ba Auwalu mukamin, sai aka ji ya karbe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng