Mahaifiya Ronaldo ta dire gefe, ta hana shi auren masoyiyarsa Georgina, ta bayyana dalilin ta

Mahaifiya Ronaldo ta dire gefe, ta hana shi auren masoyiyarsa Georgina, ta bayyana dalilin ta

  • Mahaifiyar Cristiano Ronaldo ta dire gefe tare da juya wa zakaran kwallon kafan bayan kan bukatarsa ta auren masoyiyarsa Georgina Rodriguez
  • Tsohuwar mai shekaru 66 ta sakankance cewa Georgina Rodriguez ta manne wa dan ta Cristiano Ronaldo ne saboda dukiyarsa da ta ke tatsa
  • Ronaldo da Georgina Rodriguez sun kwashe sama da shekaru 5 suna soyayya tun lokacin da kwararren dan kwallon na buga wa Real Madrid wasa

Dolores wacce mahaifiyar dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta yi fatali da bukatar dan ta na auren masoyiyarsa Georgina Rodriguez duk da kwashe sama da shekaru biyar da suka yi suna soyayya.

Cristiano Ronaldo ya kasance tare da Georgina Rodriguez suna soyayya tun ya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma an gano cewa ya na matukar jin dadin soyayyar da suke.

Read also

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

Mahaifiya Ronaldo ta dire gefe, ta hana shi auren masoyiyarsa Georgina, ta bayyana dalilin ta
Mahaifiya Ronaldo ta dire gefe, ta hana shi auren masoyiyarsa Georgina, ta bayyana dalilin ta. Hoto daga HELDER SANTOS
Source: Getty Images

Hakazalika, Georgina Rodriguez ita ce mahaifiyar karamin dan Cristiano Ronaldo kuma suna rayuwa tare a Manchester bayan komawar dan asalin kasar Fotugal din Premier League.

Kamar yadda rahotannin Marca da Remonews suka bayyana, Dolores da sauran 'yan uwan Cristiano Ronaldo sun sakankance cewa Georgina ta makale wa wanda suka dogara da shi ne saboda kudin da ta ke samu a wurinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tabbatar da cewa sun yi fatali da bukatar auren Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez.

A halin yanzu dai, shawara ta rage wa Cristiano Ronaldo da ya yi biyayya ko kuma ya jajirce domin kasancewa da masoyiyarsa Georgina.

EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, za ta daukaka kara kan hukuncin da Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotu tarayya ya yanke ta hana ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu.

Read also

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Kalu a halin yanzu sanata ne wanda aka taba yanke wa hukuncin shekaru 12 a gidan maza kan handamar N7.1 biliyan amma kotun koli ta soke hukuncin a ranar 8 ga watan Mayu.

Sai dai, kotun kolin ta bukaci a sake gurfanar da Kalu a babbar kotun tarayya. Kalu ya amfana daga wannan hukuncin inda aka sako shi daga gidan yarin Kuje, ya kuma sake mika bukata gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja da ta hana sake gurfanar da shi.

Source: Legit

Online view pixel