Rashin tsaro: Dalilin da ya sa ba za a samu zaman lafiya a kasar nan ba inji Gwamna Wike

Rashin tsaro: Dalilin da ya sa ba za a samu zaman lafiya a kasar nan ba inji Gwamna Wike

Nyesom Wike ya gabatar da lacca a makarantar National Institute for Security Studies

Gwamnan na Ribas yace sai da adalci ne za a iya samun wanzuwar zaman lafiya kasa

Wike ya nuna ya na goyon masu kiran mulki ya koma kudancin Najeriya a zaben 2023

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace maida wasu saniyar ware da ake yi yana cikin abubuwan da ke jawo matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Daily Trust ta rahoto gwamnan yana wannan bayani wajen wani taro a makarantar National Institute for Security Studies a garin Abuja a ranar Laraba.

Da yake bayani a wata lacca da aka yi wa take da “Governance, Security and Sustainable Development in Africa, Nexus, Challenges and Prospects: Rivers State as a Metaphor”, Wike ya soki shugabanni.

Read also

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Wike ya yi jawabi a makarantar NISS

An shirya wannan lacca ne ga masu yin kwas na EIMC 14 a makarantar ta NISS. A karshen wannan kwas za a ba wadanda suka yi karatun shaidar FSI.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Nyesom Wike yace gwamnatin tarayya ta gaza samar da jagoranci mai nagarta.

Gwamna Wike
Gov. Nyesom E. Wike Hoto: punchng.com
Source: UGC

“Abin da muke ji yau uzuri ne kurum, abin takaici ne. Idan ba a samun jagorancin da ke daukar matakin gaggawa, ba za a samu wani cigaba ba.”

Gwamna Wike yake cewa sai da adalci ake iya samun zaman lafiya, kwaciyar hankali da cigaba. Wike yace sai da shugabanci mai nagarta ake samun nasara.

“Ba za a samu wannan idan babu shugabanci na kwarai ba. Ba za a taba samun cigaba ba tare da shugabanci mai nagarta. Ba zai taba yiwu wa ba.”

Read also

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Jaridar ta rahoto gwamnan na Ribas yana cewa sai an samu shugabanni masu hangen nesa da bin dokar kasa, sannan gwamnati za ta iya inganta rayuwar talaka.

“Abin takaici ana cigaba da fama da matsalar shugabanci a siyasa da tattalin arziki da zamantakewar Afrika.”

Wike ya nuna goyon baya ga tsarin karba-karba, ya soki masu cewa tsarin ya saba kundin tsarin mulki. Hakan adalci ne, kuma adalci yana kawo zaman lafiya.

Dole ne mulki ya koma Kudu?

A makon nan aka ji cewa babban yaron Abubakar Tafawa Balewa ya caccaki ‘Yan siyasar Kudancin Najeriya da suke cewa dole ne mulki ya bar Arewa.

Billy Abubakar Tafawa Balewa ya na da ra'ayin cewa duk ‘Dan takarar da ya iya allonsa ya wanke a 2023, ko Bahaushe ne ko Bayarabe, muddin dai ya cancanta.

Source: Legit

Online view pixel