Farin jinin ‘Dan takara zai yi aiki a zaben 2023 ba yankin da ya fito ba inji ‘Dan Tafawa Balewa

Farin jinin ‘Dan takara zai yi aiki a zaben 2023 ba yankin da ya fito ba inji ‘Dan Tafawa Balewa

  • Abubakar Billy ya soki matsayar gwamnonin Kudu a kan batun zaben 2023
  • Babban ‘dan na Tafawa-Balewa yace ana bukatar ‘dan takara da ya cancanta
  • Billy yace la’akari da yankin da ‘dan siyasa ya fito kurum ba zai yi tasiri ba

Abuja - Abubakar Billy, babban yaron Sir Abubakar Tafawa Balewa yace akwai rauni a game da matsayar da gwamnonin kudu suka dauka game da zaben 2023.

Punch ta rahoto Abubakar Billy yana cewa ya kamata ne duk ‘dan takarar da ya samu karbuwa a gari ya zama shugaban kasa ba tare da la’akari da inda ya fito ba.

Billy ya yi wannan bayani da aka yi hira da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Channels Television.

Da yake hira da ‘yan jarida, yaron na Abubakar Tafawa Balewa yace babu dalilin da zai sa gwamnonin kudu su dage a kan cewa dole mulki ya dawo gare su.

Kara karanta wannan

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Arewa ta taba goyon bayan 'Yan kudu?

“Ba za ku ce dole ba, bai zama dole ba. Wannan alamun rauni ne.”

A cewar Billy, mutanen Arewa sun taba goyon-bayan shugabannin kudu irinsu Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan saboda ‘yan siyasa ne marasa kabilanci.

Gwamnonin Kudu
Wasu Gwamnonin Kudancin Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Dole shugaban da za ayi na gaba ya zama ya fahimci tattalin arziki domin ya fitar da kasar nan daga halin kangin tattali da rashin kudi da ta samu kanta.

“A wuri na wannan maganar karba-karbar duk siyasa ce kurum. A Najeriya muna da wasu abubuwan da suke gabanmu, ba batun wa zai yi mulki ba.
“Kamar yadda gwamnonin Arewa suka fada, babu inda doka tayi maganar karba-karba. Yarjejeniya ce da na yadda da ita, amma ba a bagas ake samu ba.”

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Billy yace dole ‘dan takarar ya nuna cancantarsa, ba kurum ya dogara da yankin da ya fito ba. Ko Bahaushe ne ko Bayarabe, babu matsala idan ya san abin da yake yi.

Babu inda ake yin haka, lallaci ne, ba a bukatar shugaba mai kabilanci, ana son wanda ya san abin da yake faru wa daga Maiduguri zuwa Bayelsa, Taraba ko Ribas.

An raba kan 'yan Arewa

Kungiyar NEF ta bakin kakakinta, Dr. Hakeem Baba Ahmed ta nuna cewa ta ji dadin matsayar da aka ji Gwamnoni 19 da Sarakunan Arewa suka dauka a taron Kaduna.

Amma kungiyar MNF tace ta na goyon bayan mulki ya je Kudu ko Arewa ta tsakiya. Shugaban MNF, Pogu Bitrus yace za a yi rigima idan mulki ya tsaya a inda yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel