Zamu fara sayar da 'Pure Water' N20: Masana'antun ruwa a jihar Nasarawa

Zamu fara sayar da 'Pure Water' N20: Masana'antun ruwa a jihar Nasarawa

  • Za'a fara sayar da Fiya-wata N20 a jihar Nasarawa saboda tsadan kaya
  • Masu masana'antun sun ce gwamnati ta kawo dauki da wuri
  • Shugaban kungiyar yayi kira da mambobinsa kada su rage ingancin ruwan da suke fitarwa

Karu, Nasarawa - Kungiyar masu masana'antun sarrafa ruwan sha na leda da gora, shiyar jihar Nasarawa ta ce mambobinta zasu fara sayar da ledan Fiya-wata N20 nan da kwanaki.

Shugaban kungiyar na Keffi-Mararaba, Usman Diggi, ya bayyana hakan ne ranar Asabar bayan taron karawa juna ilimi da akayiwa mambobin kungiyar a karamar hukumar Karu ta jihar, rahoton Premium Times.

Ya ce kungiyar ta yanke shawaran haka ne saboda kayan sarrafa ruwa sun yi tsada kuma ba zai yiwu su cigaba da sayar da ruwan leda N10 ba.

Shugaban ya kara da cewa wasu gidajen ruwa har sun fara rage ingancin ruwa a jihar saboda tsadar da kayayyaki sukayi.

Yace:

"Gwanda a kara farashin kudin fiya-wata amma a rika yin mai kyau da yin marasa inganci saboda illa ga lafiyar mutane."

Zamu fara sayar da 'Pure Water' N20: Masana'antun ruwa a jihar Nasarawa
Zamu fara sayar da 'Pure Water' N20: Masana'antun ruwa a jihar Nasarawa
Asali: Depositphotos

Ana kira ga gwamnati ta kawo dauki

Shugaban ya yi kira ga gwamnati cewa ta dau mataki na gaggawa don rage kudin kayayyaki saboda a cigaba da sayarwa mutane ruwa N10.

Ya kara da cewa:

"Kudin kilon ledar zuba ruwa da aka sayarwa N450 yanzu ya yi tashin gwauron zabi zuwa N1200, amma duk da haka muna sayar da jakar ruwa tsakanin N60 da N70."
"Asara mukeyi, dalilin da yasa wasu mambobinmu ke rage inganci kenan don cigaba da aiki."

Mr Diggi ya cigaba da cewa kungiyar na iyakan kokarinta wajen hana mutane rage ingancin ruwa yayinda take kira ga gwamnati ta kawo dauki.

Ya ce da yawa cikin mambobinsu sun kulle masana'antunsu saboda tashin kudin kaya da kudin haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel