Kashe-kashe: Fafaroma yayi magana a kan Najeriya, ya nemi Buhari ya kare al’umma

Kashe-kashe: Fafaroma yayi magana a kan Najeriya, ya nemi Buhari ya kare al’umma

  • Fafaroma Francis ya yi tir da munanan hare-hare da aka kai a kauyukan Kaduna
  • Shugaban mabiya Katolika a fadin Duniya ya yi wa wadanda suka mutu addua’a
  • A jawabin da ya fitar a Vatican, Fafaroman ya yi kira ga hukuma ta kare mutane

Vatican - A ranar Laraba, Fafaroma Francis yayi tir da harin da aka kai a kudancin jihar Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40.

Fafaroman wanda shi ne shugaban mabiya darikar katolika a Duniya, ya yi addu’a ga wadanda harin ya shafa, ya kuma yi kira ga hukuma ta tashi tsaye.

Vatican News tace Fafaroman ya bayyana kashe-kashen da aka yi da rashin hankali, ya bukaci gwamnatin tarayya ta san yadda za tayi, ta kare ran jama’a.

Jawabin Fafaroma

“Na samu labari maras dadi na ‘yan bindiga da suka kai hari a ranar Lahadin da ta gabata, a kauyukan Madamai, Abun, a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

“Ina addu’a ga wadanda suka mutu da wadanda suka samu rauni a karshen makon jiyan, da daukacin mutanen Najeriya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Fafaroma
Ana yi wa Najeriya addu'a a fadar Fafaroma Hoto: www.vaticannews.va/en
Asali: UGC

Fafaroma yana so a dauki mataki

“Ina fata za a dage wajen kare rayukan al’umma.”

A jawabinsa, Fafaroma ya nemi a dauki mataki domin kare duk wani ‘dan Najeriya a ko ina yake.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta fitar da rahoto jiya, Fafaroma Francis yayi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo karshen matsalar tsaro.

Limamin na Kiristoci mabiya darikar katolika yace ba a kudancin Kaduna kadai ake hallaka Bayin Allah ba, yace ana fama da matsalar tsaro a fadin kasar.

A ‘yan shekarun bayan nan, mutanen yankin Arewacin Najeriya na fuskantar mummunan rashin tsaro, musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da Neja.

An kashe mutane a Zaria

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga

A karshen makon da ya gabata ne 'Yan bindiga suka kashe mutane biyu, sannan suka yi garkuwa da wani malamin tsangaya a yankin Kuregu da ke garin Zariya.

Wani mazaunin garin Kuregu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da wannan harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel