Karon farko, Hotunan Mata sun yi fareti a bikin tunawa da ranar Saudiyya
- An yi bikin tunawa da kafa kasar Saudiyya ranar 23 ga Satumba
- Wannan karon ba'a bar mata a baya ba yayinda aka dama da su
- An fara murnar wannan rana ne a shekarar 2005 lokacin mulkin Sarki Abdullah
Karon farko a tarihin Kasar Saudiyya, mata a kasar Saudiyya sun yi musharaka a bikin tunawa da ranar kafa kasar ta Saudiyya.
Ana murnar ranar Saudiyya ne kowace 23 ga Satumba shekara domin murnar ranar da aka canza sunan kasar daga Masarautar Najd da Hijaz zuwa Masarautar Saudiyya.
A cewar Wikipedia, tsohon Sarkin Saudiyya Abdul Aziz Al Saud ne yayi hakan a shekarar 1932.
Sannan a 2005, Sarki Abdullah ya alanta ranar matsayin ranar murna ga al'ummar kasar
Ana bukukuwa a ranar da wakoki, rawa, faretin Sojoji, da faretin jiragen sama.
Hakazalika ana sauya cikin biranen kasar da tutotin Saudiyya iri-iri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun da aka fara murnar ranar a 2005, wannan shine karo na farko da mata zasuyi musharaka.
Gwamnatin Saudiyya ta yaye Sojoji Mata karon farko a tarihi
Gwamnatin kasar Saudiyya, karon farko a tarihi, ta samu Sojoji mata inda ta yaye sabbin dakarun Sojojin kasar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2021.
An shirya taron yaye Sojojin ne bayan sun kammala horon makonni 14 da suka fara tun ranar 30 ga Mayu, rahoton Saudi Gazette.
Shugaban sashen horo da ilimi na hukumar Sojin kasar, Manjo Janar Adel Al-Balawi; yace cibiyar ilimin na bada horo na kwarai ga Sojoji Mata.
A cewarsa:
"Cibiyar na da manufa mai muhimmanci, wacce itace bada horo da ilimi kwarai kamar yadda akeyi a kasashen duniya ga Sojoji mata."
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Kwamandan cibiyar horon Sojoji matan, Cif Sajan Suleiman Al-Maliki, Manjo Janar Hamid Al-Omari, da sauran manyan Sojojin kasar.
Asali: Legit.ng