Gwamnatin Saudiyya ta yaye Sojoji Mata karon farko a tarihi

Gwamnatin Saudiyya ta yaye Sojoji Mata karon farko a tarihi

  • Saudiyya ta samu Sojoji mata a tarihin hukumar Sojin kasar
  • Wannan na daga cikin sabbin tsarin Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya kirkiro
  • A makonnin baya, Sheikh Sudais ya nada mata cikin kwamitin gudanar da Masallatan Makkah da Madina

Riyadh - Gwamnatin kasar Saudiyya, karon farko a tarihi, ta samu Sojoji mata inda ta yaye sabbin dakarun Sojojin kasar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2021.

An shirya taron yaye Sojojin ne bayan sun kammala horon makonni 14 da suka fara tun ranar 30 ga Mayu, rahoton Saudi Gazette.

Shugaban sashen horo da ilimi na hukumar Sojin kasar, Manjo Janar Adel Al-Balawi; yace cibiyar ilimin na bada horo na kwarai ga Sojoji Mata.

A cewarsa:

"Cibiyar na da manufa mai muhimmanci, wacce itace bada horo da ilimi kwarai kamar yadda akeyi a kasashen duniya ga Sojoji mata."

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Kwamandan cibiyar horon Sojoji matan, Cif Sajan Suleiman Al-Maliki, Manjo Janar Hamid Al-Omari, da sauran manyan Sojojin kasar.

Mataimakin kwamandan cibiyar, Cif Sajan Hadi Al-Anezi, ne ya rantsar da Sojojin matan da aka yaye bayan sanar da sunayen zakaru cikin daliban.

A karshen taron, Shugaban Sojojin kasar, Janar Fayyad Al-Ruwaili, ya jinjinawa ma'aikatan cibiyar horon bisa wannan cigaba.

Gwamnatin Saudiyya ta yaye Sojoji Mata karon farko a tarihi
Gwamnatin Saudiyya ta yaye Sojoji Mata karon farko a tarihi Hoto: Saudi Gazette
Asali: Facebook

Saudiyya ta bude kofa ga mata su shiga harkar bada tsaro

A Febrairun 2021, gwamnatin Saudiyya ta bude kofa ga mata su shiga harkar Soja a kasar.

A cewar Saudi Gazzete, Mata zasu iya rike mukamin kurtu zuwa Sajen a hukumar Sojin kasa, na sama, na ruwa, da na makami mai linzami, da kuma na kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

Mata masu shekaru tsakanin 21 da 40 zasu iya nema.

A Karon Farko, Babban Limamin Makka Sheikh Sudais Ya Naɗa Mata Mataimakansa

A wnani labarin kuwa, kasar Saudiyya ta bayyana naɗa mata a manyan mukamai na hukumar dake kula da masallatai biyu mafiya daraja dake Makka da Madina.

A ranar Litinin ɗinnan ne kafar watsa labarai ta Al-Arabiyya tv, wadda mallakin Kasar Saudiyya ne, ta bada rahoto kan cigaban.

Matan da shugaban hukumar ya naɗa sun haɗa da Dakta Al-Anoud Al-Aboud da kuma Dakta Fatima Al-Rashoud.

Asali: Legit.ng

Online view pixel