Yadda jiga-jigan PDP a jihohin Kudu za su gwabza wajen zama Shugaban jam’iyya a zaben 2021

Yadda jiga-jigan PDP a jihohin Kudu za su gwabza wajen zama Shugaban jam’iyya a zaben 2021

  • A karshen Oktoban 2021 ne jam’iyyar PDP za ta zabi shugabanninta na kasa
  • Ana sa rai sabon shugaban jam’iyya zai fito daga yankin Kudu maso yamma
  • Ọlagunsoye Oyinlọla na cikin wadanda ake ganin zai iya lashe wannan zabe

Nigeria - Jagororin jam’iyyar PDP a kudu maso yammacin Najeriya suna tsara yadda za a tunkari zaben shugabanni na kasa da ake sa ran za ayi a Oktoba.

Daily Trust tace manyan ‘yan siyasar yankin suna tunanin yadda za a fito da sabon shugaban PDP na kasa, ba tare da an jawo rabuwar kai cikin jam’iyya ba.

Yankin kudu maso yammacin Najeriya ya yi kokarin fito da shugaban PDP na kasa a 2017, amma a karshe Prince Uche Secondus ne ya yi nasarar lashe zaben.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Jaridar tace wannan karo ana so shugaban jam’iyyar da zai gaji Uche Seconduus ya zama Bayarabe.

Inda gizo ke sakar

Matsalar da ake fuskanta shi ne rashin hadin-kai daga ‘yan siyasan bangaren kudu maso yamma. Kai ya ki hadu wa a kan ‘dan takarar da za a mara wa baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiga-jigan PDP
Atiku da PDP wajen kamfe a Legas Hoto: punchng.com
Source: UGC

Rahoton yace a Legas kawai akwai sabani tsakanin tsohon mataimakin shugaban jam’iyya, Olabode George da tsohon ‘dan takarar gwamna, Jimi Agbaje.

A halin yanzu sunayen da suke yawo daga Ekiti, Ondo, Ogun, Ogun da kuma Legas sun kunshi; Eyitayo Jegede; Ọlagunsoye Oyinlọla da kuma Ayodele Fayose.

Takarar Prince Olagunsoye Oyinlola

Ana rade-radin gwamnan Oyo, Seyi Makinde, yana goyon bayan Prince Olagunsoye Oyinlola a zaben.

Prince Olagunsoye Oyinlola ya rike mukamin sakataren jam’iyya na PDP na kasa kafin a tsige shi. Amma har yanzu bai fada wa Duniya cewa zai shiga takara ba.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Seyi Makinde ne kadai gwamnan jam’iyyar PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya. Rahoton yace babu wani daga jihar Ogun da yake harin kujerar.

PDP da zaben 2023

A ranar Litinin aka ji cewa Sanatocin Jam’iyyar PDP suna so a bar kofar neman takara a bude. Hakan na nufin babu batun a ware wa wani yanki kujera a 2023.

Ana rade-radin cewa ‘Dan Arewa za a ba tutar neman zaben Shugaban Najeriya a PDP. Haka zalika za a bar mutumin kudu ya zama shugaban jam'iyya na kasa.

Source: Legit

Online view pixel