An ga fastoci suna yawo ta ko ina, ana kiran Osinbajo ya yi takarar Shugaban Najeriya a 2023

An ga fastoci suna yawo ta ko ina, ana kiran Osinbajo ya yi takarar Shugaban Najeriya a 2023

  • Mutanen garin Osogbo sun tashi a makon nan da hotunan takarar Yemi Osinbajo
  • Kungiyar Osinbajo for All volunteer group ta dauki nauyin lika fastocin a Osogbo
  • Magoya bayan Yemi Osinbajo suna so ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023

Osun - A ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, 2021, fastocin takarar zaben 2023 dauke da hotunan Farfesa Yemi Osinbajo, suka fara yawo a jihar Osun.

Punch ta fitar da rahoto cewa hotunan mataimakin shugaban kasar sun bayyana a muhimman wurare garin Osogbo, jihar Osun, a farkon makon nan.

Ba a bayyana kujerar da mataimakin shugaban Najeriyar zai nema a zaben na 2023 ba, amma fastocin duk suna dauke da taken ‘Osinbajo for all 2023.’

Jaridar tace an dauki hoton Farfesa Osinbajo yana sanye da bakar kwat. Wata kungiya ta ‘Osinbajo for All volunteer group’ ta dauki nauyin fastocin.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Mazauna garin na Osogbo sun ga hotunan a yankuna irinsu Oke Onitea; Lameco Junction; Dele Yes Sir junction; Abere Bus stop, da Ilesa Garage Junction.

Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo Hoto: www.pulse.ng
Source: UGC

Mazauna sun tashi sun ga hotuna

An kuma buga fastocin a Oke Bale Junction da kofar shiga fadar Sarkin Ataoja da ke Osogbo.

Bisa dukkan alamu magoya bayan mataimakin shugaban kasar sun bata dare ne sun lika hotunan. Mutane sun tashi a safiyar ranar Litinin da fastocin.

Mazauna babban birnin Osogbo sun shaida wa manema labarai cewa babu wanda ya ga wadannan fastoci har zuwa yammacin Lahadin da ta gabata.

Su wanene suka lika fastocin?

Da manema labarai suka tuntubi shugaban kungiyar magoya-bayan, Osinbajo for All Volunteer Group, Peter Ogundeji, yace sune suka cika ko ina da fastocin.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Sai dai Peter Ogundeji yace Yemi Osinbajo bai umarce su da su fara yi masa yakin neman zabe ba. Har yanzu Osinbajo bai fada wa kowa zai yi takara a 2023 ba.

Shehu Sani ya tabo batun 2023

Shehu Sani yace tsari na karba-karba zai taimaka wajen kawo adalci. Sanatan yana ganin idan Kudu suka ce da barazana za su yi amfani, to ba za su dace ba.

A wata hira ta musamman, tsohon 'dan majalisar ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa ba don bangaren Yarbawa ba, da Buhari bai zama shugaban kasa ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel